Gwamnatin Kasar Jamhuriyar Nijar ta haramta wa ’yan Najeriya masu sana’ar tukin tasi a kasar su sama da 200 ci gaba da aiki sai kowannensu ya biya ta harajin N700,000.
Sabuwar Dokar Sufuri ta wajabta w duk wani dan Najeriya da ya yi gudun hijira zuwa Nijar da ke son ci gaba da haya da motarsa mai dauke da lambar Najeriya, mallakar wata ’yar takarda kan kudin kasar 600,000 CFA, kwatankwacin N700,000.
- Hana mata aikin jinkai ta haifar wa MDD tsaiko a Afghanistan
- Mutum 7 sun mutu, 53 sun jikkata a gobarar gidan caca a Thailand
Wadanda lamarin ya shafa da ke zama a Diffa a kasar, sun koka kan wanna batu, tare da rokon hukumomin Najeriya da na Nijar su shigo cikin lamarin don samun maslaha.
Malam Musa Abdullahi, dan asalin Karamar Hukumar Abadam a Jihar Borno ne, kuma shugaban ’yan Najeriya masu sana’ar tukin tasi a Diffa.
Ya ce, ’yan sanda da kwastam sun kwace musu motoci kusan 100 a mako guda saboda sabuwar dokar.
Ya kara da cewa, kudin da aka bukaci su biya din ya zarce kudin da yawancin motocin da suke haya da su don neman abin da za su ci da iyalansu.
Cikin wata muryarsa da aka nada aka yada, Shugaban Kungiya Masu Motoci a Diffa, Alhaji Gali Mustapha ya ce, dole wadanda lamarin ya shafa su gabatar da inshorar ECOWAS da sauran muhimman takardu kafin a sahale musu ci gaba da aiki a kasar.
Sai dai a nasu martanin, wasu mambobin kungiyar sun zargi shugaban kungiyar da haifar da rudani a Diffa.