Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya ce shugaba Buhari ba shi da masaniyar ’yan bindiga sun yi barazanar sace shi, har sai da ya fada masa.
Ta cikin wani shirin gidan Radiyo a Najeriya, El-Rufa’in ya ce kimanin shekara biyar ke nan yana bawa Gwamantin Tarayya shawarar bin ’yan ta’adda har maboyarsu a bude musu wuta, domin a ganinsa shi ne kadai abin da zai magance matsalar, amma gwamnatin ta yi burus da shi.
- Barazanar Sace Buhari Abin Dariya ne – Lai Mohammed
- Tsige Buhari: Sanatoci sun raina hankalin ’yan Najeriya —Garba Shehu
“Na samu labarin bidiyon da ’yan bindiga suka saki suna barazanar sace Buhari da ni.
“Ta yaya za mu zama a kasar da ke da tarin jami’an tsaron Sojoji da ’yan Sanda da kuma karfin Gwamnatin Tarayya amma a ce wai ’yan bindiga na barazanar sace shugaban kasa?
“Idan gwamnatocin da suka shude sun dauki abin wasa don suna ganin yana faruwa ne a Zamfara da Katsina da Kaduna da Neja, to yanzu ya zo har inda muke.
“Don haka dole mu tashi tsaye domin kawo karshen mutanen nan; shi ya sa ma na je na samu Shugaban ranar Lahadi don tattauna wadannan matsalolin.
“Na kuma sanar da shi barazanar da aka yi mana a bidiyon ’yan ta’adda, a lokacin ne ma ya sanr da ni ba shi da labari”, in ji shi.
El-Rufai ya ce Shugab Buhari ya tabbatar masa cewa ya yi zaman tattaunawa na musamman da masu ruwa da tsaki kwanaki hudu da suka gabata kafin haduwarsu da gwamnan ranar Lahadin, kuma ya ba su umarnin amfani da karfin aikinsu su kawo karshen matsalar.
“Muna fatan da yardar Allah sojoji da ’yan sandan da shugaban ya bawa wannan umarnin za su hanzarta su yi abin da aka ce.
“Bai kamata mu jira wai sai sun kai farmaki ba sannan mu yi wani abu,” in ji.