✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ni ma kudin nake nema

Wani barawo ne ya hau babur din wani dan acaba, ashe ba ya da kudi, suna cikin tafiya sai da suka zo kusa da wata…

Wani barawo ne ya hau babur din wani dan acaba, ashe ba ya da kudi, suna cikin tafiya sai da suka zo kusa da wata makabarta sai barawon ya ce da dan acaba, a nan zai sauka, domin shi fatalwa ne. Sai dan acaban ya bi shi cikin makabartar domin ya karbi kudinsa. Suna zuwa sai barawon ya ce wane idan kana cikin kabarin nan, ka ba ni Naira ashirin na biya dan acaba. To ashe bai sani ba, akwai wani mahaukaci a kwance a kusa da wani kabari, nan take mahaukacin ya amsa ya ce: “Wallahi ni ma kudin nake nema!” Su biyun sai suka ruga a guje.
Daga Isah Ramin Hudu, Hadeja.