✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ni ce mace ta farko a sashin Hausa na BBC – Delu Abubakar

Hajiya Delu Abubakar Usman ita ce mace ta farko da ta fara aiki a sasahin Hausa na BBC, a zantawarta da Aminiya ta bayyana irin…

Hajiya Delu Abubakar Usman ita ce mace ta farko da ta fara aiki a sasahin Hausa na BBC, a zantawarta da Aminiya ta bayyana irin tsangwama da ta fuskanta a sanadin hakan, ta kuma yi bayani a game da bambancin katsalanda da ’yan jarida ke fuskanta a nan Najeriya da kasashen da suka ci gaba.

Aminya: Za mu so ki gabatar da kanki.
Delu Abubakar Usman: Sunana Delu Abubakar Usman, an haife ni a Birnin Kebbi (Jihar Kebbi) a ranar 14 ga Afrilun 1960. Na fara karatu a firamaren Santaral da ke Birnin Kebbi na karasa a firamaren Turaki da ke Sakkwato. Na yi Kwalejin Horar da Malamai Mata (WTC) ta Birnin Kebbi na gama a 1976, daga nan sai na je Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Sakkwato, sai Kwalejin Ilimi ta Sakkwato a tsakanin 1979 zuwa 1983, bayan nan sai na yi aikin yi wa kasa hidima a Makarantar Firamare ta Model da ke Sakkwato.
Daga nan na wuce Jami’ar Usman dan Fodiyo da ke Sakkwato a 1984 zuwa 1987, bayan nan sai na samu aiki da Hukumar Samar da Ayyukan yi ta kasa (NDE) a Abuja, a 1987 zuwa 1990. Ana cikin haka sai na ga sanarwa a jarida ana neman ma’aikata a sashin Hausa na BBC, sai na rubuta takardar neman aiki, an kira mu Kaduna muka yi jarrabawa a lokacin shugaban sashin Hausa na BBC, Mista Barry Barges ya zo Najeriya, daga bisani sai a ka kira ni aka sanar da ni cewa na yi nasara. Sai na wuce Landan na kasance mace ta farko da ta zamo ma’aikaciya a sashin, na yi aiki a wajen daga 1990 zuwa 1993.
Aminiya: To dama kin karanta aikin jarida ne ko aikin kafin zuwanki can?
Delu Abubakar Usman: A gaskiya ban taba aikin jarida ba a lokacin, ban kuma karanta aikin ba, darasin da na karanta a makaranta Turanci ne ba Hausa ba, sai dai ina da sha’awar aikin kuma ina ganin zan iya idan na samu dama, a can na fara har na samu karbuwa, kuma har yanzu ina da sha’awar aikin.
Aminiya: To yaya aikin ya kasance miki?
Delu Abubakar Usman: To dama idan a ka dauke ka aiki a BBC a matsayin cikakken ma’aikaci za a saka aiki ta ko’ina don ka samu damar gogewa a aikin, za ka yi gabatarwa, za ka yi labarai, za ka yi shirye-sherye da sauran fannoni. To da muka tafi a haka muka faro, kuma ko ka iya rubutun tafureta ko ba ka iya ba, dole ka koya saboda da shi ne za ka yi rubutu. Kai za ka zakulo labarai ka fassara sannan ka je cikin sutudiyo ka gabatar.
Aminiya: Yaya za ki bayyana aikinku a lokacin da kuma a yanzu?
Delu Abubakar Usman: Hakika an samu sauyi sosai, an samu sauye-sauyen fasaha da zamani ya kawo, kamar yadda na gaya maka a lokacin da muka yi aikin, mun yi amfani ne da keken rubutu (tafureta), na yanzu kuma kwamfuta ce ake rubutu da ita, koda yake daga bisani mu ma mun koma kwamfutar amma dai ingancinsu bai kai irin na yanzu ba, kuma akwai sauye-sauye da dama da ci gaban fasaha ya kawo a yanzu, wanda suke taimakawa wajen ingantawa da kuma aiwatar da aiki cikin sauki.
Aminiya: Kamar wadanne abubuwa ne suka burge ki a lokacin da ba za ki manta ba?
Delu Abubakar Usman: Abubuwan suna da yawa, sai dai muhimmai a cikinsu shi ne ba da damar aiki da suke yi ba tare da takurawa ba, komai na cikin tsari kowa ya san rana da lokacin aikinsa, dama akwai jadawalin aiki da ake tsarawa mako-mako tun ranar Juma’a idan ka shigo za ka gani wanda shugaban sashin Hausa na BBC ke tsarawa, yau wannan ne da labarai wancan kuma zai gabatar, wannan ne da rahoto, ba matsalar abin hawa bare latti, su kansu masu tukin tasi suna aikinsu a tsanake, haka nan idan ka shigo gidan bangarori kamar na injiniya masu kula da na’urori, ko laburari, ko dakin abinci, kowa na aikinsa cikin ka’ida. Idan wani abu ne ya samu matsala kana buga waya sai a zo a kawo maka dauki, in na gyarawa ne a gyara, in na sauyawa ne a sauya, aiki dai akwai dadi ba takura ko kadan.
Sannan ba a kama kafa ko nuna girma a can da karamin ma’aikaci da babba da ma shugaba duk idan aka hadu, za a yi raha ba tare da nuna daukaka ba, alal misali idan na hadu da shugaban sashin Hausa zan kira sunansa Barry, shi kuma ya ce Delu, haka zan yi da na kasa da ni ni ma, ba wani ranka dade ko Hajiya, haka dai ake aikin tamkar abokai, to wannan na sa a saki jiki da juna a gudanar da aiki cikin tsanaki da walwala.
Aminiya: A bangaren takaici fa ko akwai wani abin da za ki iya tunawa?
Delu Abubakar Usman: To ba zan ce takaici haka nan ba, sai dai na ce wani abu da ya dan daure mini kai haka, ko ma in ce bajinta. Wato a lokacin da na je wajen, kasancewata ni ce mace ta farko a Sashin Hausa, sutura irin namu na gida da na ke sanyawa a koyaushe wanda ya zamo bakon abu a wajen abokan aiki Turawa, ya mai da ni abin kallo da kuma burgewa, har ta kai an dauki labarin a Mujallar BBC ta cikin gida don ma’aikatan wajen, inda aka sako ni a labari ga wata ’yar Afirka da ke sanya sutura irin nasu ta bayyana a BBC kuma abin na burge Turawa. To ni a wajena bai sani wani takaici ba ko kadan, ammai sai wata kungiyar mata da ke kula da hakkoki da kare muradun mata, ta nuna taKaicinta a kai har ta kwabi jaridar na yin labarin wanda ta bayyana a matsayin tsangwama, sun nuna cewa aikin mutum ya kamata jaridar ta ba muhimmanci ba maida hankali a kan al’amura kamar suturarsa ba. A kan hakan wasu ma sun tambaye ni, ko ni ce na kai korafi ga kungiyar matan, na ce masu a’a. A lokacin ina bakuwa a wajen ni ban ma bai wa al’amarin muhimmanci ba, sai daga bisani ne nake tunawa da kungiyar na nuna kulawarsu a gare ni da jiin takaici a madadina.
Aminiya: Wadanne ma’aikata ne za ki iya tunawa da kin yi aiki da su?
Delu Abubakar Usman: Lokacin da na je na samu Usman Muhammed akwai Umar Yusuf karaye da Isa Abba Adamu da Adamu Aliyu Kiyawa da Salisu Saleh Na’inna dambatta da Sulaiman Ibrahim Katsina da Yusuf Nagi Ahmed. Akwai kuma Saleh Halliru da Abubakar Kabir Matazu dama tare aka dauke mu aiki, sai kuma Balkisu Labaran da Chrinstina Sisi wadanda suka zo ina can.
Aminiya: Ina kika koma bayan kin bar BBC?
Delu Abubakar Usman: Dama an dauke ni aiki ne na tsawon shekara biyu, bayan nan sai aka sabunta aikin da karin shekara guda, to da na cika shekarar sai na bar wajen ban nemi kari ba su kuma ba su min tayi ba. To bayan dawowata Najeriya kasancewar ina da sha’awar aikin jarida, sai na nemi aiki a Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna, har sun ba ni aikin, sai na sake shawara ban karba ba, dalili shi ne ganin a baya ana jina a BBC ga kuma walwalar aiki a wajen ba katsalanda, nan kuma da zan koma yanzu ba ni da tabbaci a kan wadannan al’amura, don ban san yadda suke yin na su ba, sai na hakura da aikin, ban karba ba.
Aminiya: Duk da cewa ba ki yi wani aikin jarida a nan gida ba, ya kike ganin bambancin aiki a tsakanin nan da waje?
Delu Abubakar Usman: A gaskiya akwai bambanci wajen katsalanda, nan dai na san akwai wasu labaran da ba dama ka yi su a kafafen yada labarai na hukuma, wani zubin ma har na masu zaman kansu, komai muhimmancin labarin da kuma wahalar da aka sha wajen samo shi sai a kashe, saboda labarin ya tabo wani abu da shugabannin wurin ko masu wurin, ba sa so a tabo. Saboda kusancinsu da wadanda labarin ya shafa ko suna tsoron matsalar da zai haifar idan aka bayyana shi. Can kuwa kai ne za ka ga labari da aka yi shi a sashin Turanci, amma saboda rashin sha’awarsa ko muninsa ga masu sauraronku dalilin al’ada, sai ka ki, misali auren jinsi da makamantansu. To su kafofin yada labarai na wadancan kasashe sun fi so matukar labari ya zo a babba, to a dauke shi a karanta shi a kowane sashi, kada a yi watsi da shi, duk da dai ba tursasa muku za su yi lallai sai kun yi shi ba. Ka ji bambancin katsalanda aikin jarida a tsakanin na nan gida da na waje.
Aminiya: To bayan kin ki karbar aiki da Rediyon Najeriya na Kaduna wane aiki kika koma?
Delu Abubakar Usman: To bayan na nemi aiki da rediyo Najeriya Kaduna na samu amma ban karba ba saboda dalilan da na zayyana, sai na samu aiki da Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa (Maritime Authority) da ke Legas, na shekara kamar biyu a wajen. Sai kuma na samu aiki da Ma’aikatar Mata ta Tarayya a nan Abuja, a matsayin Mataimakiyar Darakta na zama Darakta a ma’aikatar, sai dai sakamakon tsarin gwamnati na idan ka cika shekara takwas a mukamin Darakta ko Babban Sakatare sai ka ajiye aiki, wannan ya sa na ajiye aikin a shekara ta 2010. Sai dai a lokacin da nake aikin, na halarci makarantar nan ta manyan jami’an gwamnati (NIPSS) da ke Kuru kusa da Jos daga shekara ta 2008 zuwa 2009.
Aminiya: To a bangaren iyali fa?
Delu Abubakar Usman: Allah Ya yi wa maigidana rasuwa a 1984, kuma mun samu ’ya’ya biyu namiji da mace, Hafiz da Rafi’a, shi Hafiz ya yi aure har ya samu da, ita kuma Rafi’a lauya ce tana aiki da Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya a nan Abuja.