✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Neymar zai fara yajin aiki a PSG

Shahararren dan kwallon Brazil da yanzu haka yake buga wa kulob din Paris Saint Germain (PSG) na Faransa kwallo, Neymar ya ce zai shiga yajin…

Shahararren dan kwallon Brazil da yanzu haka yake buga wa kulob din Paris Saint Germain (PSG) na Faransa kwallo, Neymar ya ce zai shiga yajin aiki muddin kulob din ya ki yarda ya sayar da shi ga tsohon kulob din sa na FC Barcelona na Spain.

Neymar wanda ya canja sheka daga kulob din Barcelona zuwa na PSG a shekarar 2017 a kan Fam miliyan 199 (kimanin Naira biliyan 93 da miliyan 729), hankalinsa ya sake karkata ne zuwa tsohon kulob din da ya bari kimanin shekara uku da suka wuce.

Jaridar Mundo Deportibo ta Spain ta ce tuni Neymar ya fara neman gidan haya a garin Barcelona a kokarin da yake yi na sake komawa can. Sai dai ya zuwa hada wannan rahoto kulob din PSG da na FC Brcelona ba su cimma matsaya game da sayar da Neymar ba.

Neymar dai ya yi barazanar kaurace wa samun horo a kulob din PSG a makon gobe, muddin kulob din ya ki amince masa ya koma Spain.