✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NEMA ta kai gudunmawa wasu asibitoci 3 a Kano

NEMA ta rubanya kokarin da Gwamnatin Kano ke yi wajen share hawayen wadanda suka fuskanci bala'o'i.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta bayar da gudunmawar magunguna da kayayyaki ga wasu asibitoci uku a Jihar Kano, domin tallafa wa mutanen da bala’io’i daban-daban ya shafa.

Babban Daraktan NEMA, Mustapha Habib ne ya gabatar da kayayyakin, inda ya ce tallafin na daga cikin kokarin Gwamnatin Tarayya na tallafa wa mutanen da fashewar tukunyar gas da sauran bala’o’i suka aukawa.

Daraktan wanda shugaban Hukumar na Kano da Jigawa, Dokta Nuraddeen Abdullahi ya wakilta, ya ce asibitocin da suka samu tallafin sun hada da Asibitin Kwararru na Murtala, da na Duba Gari da ke unguwannin Ja’en da Sharada.

Kayayyakin da aka raba sun hada da katan 10 na kayayyakin karin ruwa, da sinadarin wanke hannu na da kashe kwayoyin cuta, allurai da sauran magunguna da kayyakin jinyar marasa lafiya.

A nasa banagren Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Aminu Tsanyawa ya ce tallafin zai taimaka wajen bunkasa harkar lafiya a jihar, kasancewar kari ne kan Naira miliyan 15 da gwamnati ta kashe wajen samar da makamantan kayayyakin.