Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da sako sakamakon jarrabawar NECO na daliban Jihar, wanda a baya aka rike saboda taurin bashin gwamnati.
Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO) dai ta rike sakamakon daliban da ke makarantun gwamnati a Jihar, duk da sakin na takwarorinsu a wasu jihohin, saboda bashin da hukumar ke bin ta, wanda ya kai kusan Naira biliyan daya da dubu dari takwas.
- Sudan: Sojoji sun dawo da fira Minista Hamdok kan mulki
- Harin ’Yan tawayen Kamaru: An kashe mutum 13, wasu 20 sun bata – Mazauna Taraba
To sai dai a cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimin Jihar ta fitar ta hannun kakakin ma’aikatar, Aliyu Yusuf, Gwamnatin ta ce yanzu daliban za su iya duba sakamakon saboda an cimma matsaya.
A cewarta, “Sakin sakamakon, kamar yadda Kwamishinan Ilimin Jihar, Muhammad Sanusi Kiru ya tabbatar, zai taimaka wa dalibai su sami guraben karatu a jami’o’ii da sauran manyan makarantu.
“Saboda haka, muna kira ga dalibai da su yi amfani da katinsu wajen dubawa da kuma fitar da sakamakon jarabawar, tare da yin kira ga dalibai da su yaba wa gwamnati kan kokarin da take yi, duk kuwa da karancin kudaden da take fama da shi.
“Muna kuma jaddada aniyar Gwamnatin Jihar Kano kan ci gaba da tallafa wa bangaren ilimi da bashi fifiko,” inji sanarwar.