Hukumar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi (NDLEA) za ta fara sanya kyamarori a jikin jami’anta domin inganta aikinsu.
Shugaban hukumar, Mohamed Buba Marwa, ya bayyana haka ne a wani taro a Abuja inda aka yi wa wasu jami’ai karin girma a ranar Laraba.
Marwa ya ce, “Za mu sa kyamarori a jikin jami’anmu a lokacin gudanar da muhimman ayyuka don tabbatar da amincinsu da kuma ingancin ayyukan.”
Don kara inganta aikin hukumar, Marwa ya bayyana cewa NDLEA na kafa rassa biyar a Legas da Abuja.
- Tubabbun ’Yan Boko Haram 560 Sun Fara Koyon Sana’o’i A Borno
- An kama wani da ƙoƙon kan mutum a Abuja
Hukumar ta kara wa jami’anta 5,042 girma, ciki har da manyan hafsoshi biyu zuwa mukamin mataimakin kwamanda-janar.
Marwa ya ce karin girma ya biyo bayan tsauraran gwaje-gwaje da aka yi wa jami’an, yana mai bayar da tabbacin inganta yanayin aikin jami’an hukumar.