Jami’an Hukumar Yaki da Safarar Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) sun kama sama da kilo 24,311 na Hodar Iblis da maganin codeine da kuma samfurin Arizona da Colorado na Tabar Wiwi.
An kama kwayoyin ne a wani sabon samame da Hukumar ta kai a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja, da kuma Tashar Jiragen Ruwa ta Tincan da ke Apapa, dukkansu a Jihar Legas.
- Yadda Na Kirkiri Yin Shayi A Tanki Da Bututu – Rabilu Mai Shayi
- Ba Daidai Ba Ne A Katse Hanyoyin Sadarwa A Zamfara Da Katsina – SERAP
Hakan na faruwa ne kusan mako guda bayan hukumar ta cafke kwayar Amphetamine wadda kudinta ya kai Naira biliyan shida a tashar jiragen ruwa ta Apapa.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya ce ranar Juma’a aka kama kashin farko na miyagun kwayoyin wanda ya kunshi sama da kilo 10 na Hodar Iblis din da sama da kilo 25 na tabar wiwi daga Afirka ta Kudu.
Ya kara da cewa a wani jerin samame tsakanin Asabar, hudu ga watan Satumba zuwa Litinin 6 ga watan Satumban 2021 a sassa daban-daban na Legas, an kama mutum hudu da ake zargi da safarar miyagun kwayoyin.
Ya ce, “A tashar Jiragen Ruwa ta Tincan, jami’an Hukumar sun kama wata kwantena mai tsawon kafa 40 dauke da maganin tari mai sinadarin Codeine ranar Litinin, shida ga watan Satumba bayan samun bayanan sirri daga abokan huldar Hukumar na kasa-da-kasa.
Mai alawar wiwi
“An kuma samu kilo 4,020 na kwayoyin maganin radadi da katan 47 na kwanuka masu rike zafi wadanda aka yi amfani da su don boye miyagun kwayoyin – duk daga Indiya aka shigo da su.
“Haka kuma, an kama tabar wiwi ’yar Colorado a cikin wata mota kirar Dodge Grand Caravan wadda aka shigo da ita daga Kanada a cikin wata kwantena mai tsawon kafa 40 ranar Juma’a 10 ga watan Satumba,” inji Mista Babafemi.
Bugu da kari, a Abuja, an kama wata budurwa mai shekara 20 da haihuwa tana sayar da alawa da biskit masu kunshe da miyagun kwayoyi.
An kuma kama mai kai mata kayan ga masu saye, wani matashi mai shekara 27.
An kama su ne a gundumar Garki Area 11 ranar Juma’a 10 ga watan Satumba da wasu daga cikin kayan nasu masu kunshe da kwayoyi da kuma giram 400 na tabar wiwi ’yar Arizona. A cewarsu sun yi fiye da shekara guda suna wannan sana’a.
A Jihar Edo kuma an kwace kilo 1,425 na curarriyar tabar wiwi a wani samame da aka kai a wajen garin Aviosi, kusa da Uzebba, a Karamar Hukumar Owan ta Yamma ranar Litinin 6 ga watan Satumba.
Ta koma ruwa
A wannan ranar ta Litinin kuma dai an kama wani matashi a hanyar Zariya zuwa Danja, a Jihar Kaduna, da kilo 10 na Tramadol da kilo 60 da rabi na Exol-6.
Kwana guda kafin nan kuma an kama wani bawan Allah da kilo 44 na tabar wiwi a unguwar Tudun Wada ta birnin Jalingon Jihar Taraba.
Hakazalika jami’an NDLEA a Jihar Kwara sun kama wata mata wacce kwanan nan ta kammala zaman kason da Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Ilori ta tura ta bayan ta same ta da laifin ta’ammali da giram 22 na hodar cocaine.
Kamun na baya-bayan nan ya biyo bayan samun bayanan sirri ne cewa ta ci gaba da sayar da hodar ta cocaine a kwaryar birnin Ilori.
A Gombe ma, jerin samamen da aka kai a fadin jihar a tsakanin ranar Laraba 1 ga watan Satumba da Juma’a 10 ga wata ya kai ga kame dillalan kwayoyi akalla tara wadanda aka samu miyagun kwayoyi iri-iri masu nauyin kilo 150 a wurinsu.
A daya daga cikin jerin samamen, an kama wata babbat mota kirar DAF makare da kwayoyi masu sa maye wadanda nauyinsu ya kai kilo 128.
Motar, wadda ta fito daga garin Anaca na Jihar Anambra, an kama ta ne a hanyar Gombe zuwa Yola.