✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta cafke dillalan miyagun kwayoyi 192 a Ebonyi

NDLEA ta kama tabar wiwi da nauyin ta ya kai kilo 113.414 a jihar daga Janairun zuwa Satumba.

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ta kama sama da mutum 192 da ake zargin masu fataucin muyagun kwayoyi ne a Jihar Ebonyi.

Hukumar ta ce ta yi wannan kamen ne daga watan Janairu zuwa Satumaba na wannan shekarar da muke ciki.

Kazalika, ta ce ta samu nasarar kama tabar wiwi da nauyin ta ya kai kilo 113.414 a jihar daga Janairun zuwa Satumba.

Kwamandan NDLEA na jihar, Mista Iyke Uche ne ya bayyana haka yayin tattaunawarsu da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ranar Talata a Abakaliki, babban birnin jihar.

“Jami’anmu sun kama kayayyakin ne a wurare daban-daban a fadin jihar,” in ji shi.

Kwamandan ya kara da cewa, ta’ammali da miyagun kwayoyi ke janyo aikata manyan laifuka, don haka ya ce za su ci gaba da kokari wajen yaki da wannan matsalar har sai sun ga bayanta.

(NAN)