✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nazari da sharhin littafin Tarihin Biu

Tarihi muhimmi ne kuma ginshikin abu ne da ke tallafe da dan Adam, domin kuwa ta hanyar tarihi ne ake sanin jiya domin tafiyar da…

Tarihi muhimmi ne kuma ginshikin abu ne da ke tallafe da dan Adam, domin kuwa ta hanyar tarihi ne ake sanin jiya domin tafiyar da al’amuran yau, sannan ake tsinkayar gobe domin ta kasance mai kyau da fa’ida.
Michael Crichton, daya daga cikin masana da suka shahara a duniya, ya ce: “Idan ba ka san tarihi ba, to ba ka san komai ba. Ka kasance ganyen da bai san cewa daga jikin itace yake ba.”
Marubuci kuma masanin al’amuran rayuwa, George Orwell, shi ma ya ce: “Hanya mafi sauki da za ka iya lalata al’umma, ita ce ka hana su sani tare da goge fahimtar tarihinsu.”
Shi kuwa Confucius, wanda malamin falsafa ne da ya yi suna a duniya, cewa ya yi: “Ka nazarci tarihi, matukar kana son fahimtar gobe.”
Sanin wadannan bayanai da kuma muhimmancin da ke tattare da tarihi,  su suka sanya fitaccen marubucin nan  kuma mai kishin al’ummarsa, Dokta Bukar Usman (OON), ya kwashe tsawon shekara tara yana bincike da nazari, sannan ya rubuta tarihin mahaifarsa, Biu – tarihin da ba a rubuta kamarsa ba, tun bayan samun ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka.
Littafin, wanda aka yi masa wallafa mai inganci, dauke da hoton babban tsaunin Tilla, yana dauke da shafuka 693, an rubuta shi ne da harshen Ingilishi kuma yana dauke da sassa hudu da babi har 14, sannan akwai bayani game da marubucin da bayanan godiya da gabatarwa daga marubuci da kuma gabatarwa dangane da kunshiyar littafin. Haka kuma daga karshe, akwai shafukan karin bayani da jadawalin kalmomi da kuma rataye.
A lokacin da yake gabatarwa ga littafin a shafi na 17, kwararren malamin tarihin nan da ke Jami’ar Abuja, Farfesa Sa’ad Abubakar OFR, Ubandoman Muri, ya ce:
“Littafin Tarihin Biu ya samu ne a sakamakon cikakken nazari da binciken marubucinsa, wanda ya faro shekara takwas da suka gabata, a 2006. A cikin wadannan shekaru, masu bincike sun karade dukkan kananan hukumomi hudu da ke yankin Biu da makwabtansu, yankunan Askira, Lassa, Mubi da Shani, domin samo ingantattun bayanai ta hanyar tattaunawa da tsofaffi, domin samo adanannun kayan tarihi sun kuma duba rubutattun takardu da kuma tsofaffin hotuna. Haka kuma, an samu bayanai na kwarai daga dakunan adana littattafai da gidajen adana kayan tarihi na Borno da Kaduna. Haka kuma marubucin ya karade lungunan yankin, domin tantance wasu tsirrai da itatuwa, kuma da daukar hotunan wurare na zahiri. Daga karshe kuma, marubucin ya nazarci rumbunan adana bayanai na intanet, musamman ma na Jami’ar Florida, domin tattaro wasu karin bayanai da suka danganci tarihin Biu, domin rubuta littafin.”
A cikin Kashi na Farko, wato Kashi na A, wanda ke kunshe da babi na daya, marubucin ya bayyana dalla-dalla yanayin kasar Biu, wanda ya hada da sunayen kananan hukumomi hudu na Bayo, Biu, Hawul da kuma Kwaya-Kusar da fadinsu a murabba’in kilomita da tsaunukan da ke cikinsu da yanayin ruwan sama da suke samu da kayayyakin abinci da suke nomawa, kamar yadda ya bayyana ire-iren tsirrai da itatuwan da ke yankunan da sauransu.
Kashi na B, kuwa yana kunshe da babi biyar, daga shafi na 47 zuwa 175. Marubucin ya yi nazarin Biu kafin zuwan Turawan mulkin mallaka, inda ya kawo tarihi da salsalar asalin Daular Biu, a babi na 2. A babi na 3, littafin ya yi bayani game da asalin mutanen da suka fara zama a Daular Biu. A yayin da babi na 4 ya zayyana al’amuran mulkin gargajiya a yankin, babi na 5 kuwa ya yi bayyana irin mutanen da ke zaune a yakin da kuma irin harsunansu. Sai kuma babi na 6, inda aka yi bayani dalla-dalla na al’adun gargajiyar mutanen yankin da yadda suke tafiyar da su a rayuwa.
Yamtarawala, shi ne jarumi kuma mayakin da aka jingina wa kafa Daular Biu. Tarihinsa ya yi kama da na Bayajidda a kasar Daura da kuma Oduduwa a kasar Yarabawa.
A cikin wannan Kashi na B, marubucin ya yi bayanin yankin Biu kafin zuwan jarumi Yamtarawala da yadda bayan ya zo yankin ya zama Sarki (Kuthli) na farko a Biu. Haka ya bi diddigi ya kawo tarihin haihuwarsa da wurin da ya fito, kamar yadda ya yi bayanin irin yake-yaken da ya fafata a yankunan Biu da kewaye. Yadda aka yi aka kafa Daular Masarautar Biu, duk an bayyana dalla-dalla da yadda shi Yamtarawala ya gudanar da mulkinsa har zuwa rasuwarsa. Irin yadda ya yi amfani da ’ya’yansa a fagen fama da bayanan da suke danganta irin hatsabibancinsa na tsatsuba, duk an kawo su cikin wannan littafi cikin yanayi mai armashi.
Kamar yadda aka yi ta samun karo a tarihin jarumai irin su Bayajidda da Oduduwa, haka shi ma Yamtarawala, akwai labarun da ake dangantawa da shi, wadanda suka yi kama da tatsuniyoyi. Marubucin nan ya tantance, ya bayyana irin wadannan labarai, a shafi na 63 zuwa na 69.
Ba nan ya tsaya ba, littafin sai da ya zayyano sunaye da shekarun mulkin kowane sarki da ya mulki Biu, tun daga shi na farko, jarumi Yamtarawala, wanda ya yi mulki daga 1535 zuwa 1560, lokacin da ya rasu, har zuwa sarkin Biu mai ci a yau, Mai Umar Mustafa Aliyu; wanda ya faro sarauta daga 1989 zuwa yau.
Akwai bayanai game da kafuwar muhimman garuruwa da kabilu da ke yankin Biu, wadanda suka hada da Miringa, Mandaragrau, Kogu, Buratai, Bam, Gur, Sakwa, Kwajaffa, Kwaya Burra, Kwaya Kusar, Wawa, Zobi, Wandali, Yimirdlalang, Brihyel, Jara Nda’li, Zara, Balbaya, Wuyo, Fikahyel, Teli, Jara Gol (Gwal), Shani da kuma Lassa.
Baya ga ingantaccen bayani game da kabilun da ke Masarautar Biu, haka kuma marubucin ya zakulo wasu daga muhimman mutanen da suka yi fice a yankin. Irin wadannan mutane sun hada da Galadima Wuriwa, wanda ya rayu a tsakanin 1925 zuwa 1935 da Ya Madu Tsukurama (1925 zuwa 2013) da Ya Patum Kuru, wacce ta kai tsawon shekara 95 a yanzu da Muhammadu Ali Asura, Sarkin Dogarai, shi ma mai shekara 94. Akwai kuma Bukar Shu’aibu, wanda aka haifa a 1946, sai kuma Muhammad dankano, wanda shi kuma aka haifa a 1924.
A kashi na C, wanda ke dauke da babi  biyu, marubucin ya yi bayani ne game da Biu a karkashin mulkin Turawan mulkin mallaka.
A babi na 7 wanda ya faro daga shafi na 239 zuwa 246, an yi bayanin yadda Turawan Birtaniya suka shigo Biu da kuma yadda ta kasance bayan zuwan nasu har zuwa lokacin da aka samu ’yancin kan kasa.
A babi na 8 kuwa, wanda ya faro daga shafi na 247 zuwa 274, an yi bayani ne game da mulkin Turawa a Masarautar Biu. Marubucin bai yi kasa a gwiwa ba, sai da ya samar da bayani dalla-dalla game da salon mulkin Turawa da ake wa lakabi da Baba-na-daka-gemu-na-waje (Indirect Rule).
A kashi na D, kuma na karshe a littafin, wanda ke dauke da babi  6 (babi na 9, 10, 11, 12, 13 da 14), an yi bayani dalla-dalla ne game da Biu bayan samun ’yancin kan kasa daga Turawan mulkin mallaka.
A bisa wannan tsarin na mulkin ’yan kasa, a babi na 9, an yi bayani ne game da birnin Biu, yankunansa na mulki da kuma kananan hukumominsa.
A babi na 10 kuwa, marubucin ya bi kadin ilimin zamani, matsayinsa da yadda ya gudana a Masarautar Biu. Tattalin arziki da kasuwanci da dangoginsa, marubucin bai bar su baya ba, domin kuwa ya yi bayaninsu da yadda suke, ko suka gudana a Masarautar Biu. Bayanin haka ya bayyana ne a babi na 11 na littafin, wato daga shafi na 369 zuwa na 396.
A kowane wuri ko yanki, daga lokaci zuwa lokaci, akan samu ci gaba ko koma baya a al’amura daban-daban na rayuwa. A a babi na 12 na littafin nan, an yi bayanin irin ci gaban da aka samu ta fuskar siyasa da zamantakewar al’umma a yankin Biu.
A babi na 13, marubucin ya dauki lokaci ya yi bayani game da muhimman al’amura da suka danganci kyawawan dabi’u, tsarin rayuwar al’ummar Biu. Haka ya yi bayani game da wasannin gargajiya da na zamani da ake gudanarwa a yankin.
A babi na karshe, wato babi na 14, wanda ya faro daga shafi na 431 zuwa 492, an yi bayani ne game da wuraren bude ido da shakatawa da ke akwai a yankin Biu. Wadannan kuwa sun hada da wuraren tarihi da ke tsohuwar Biu da suka hada da bikuthla da Pelaminta da sauransu. A Miringa, akwai tsohuwar Rijiyar Miringa da Gidan Lawan Miringa da kuma kayayyakin fasaha na Yamtarawala da sauransu. A yankin Sakwa, akwai wuraren bude ido da suka hada da Kogin Tilla da kauyen Chata da Gidan Hutawa na Turawa da sauransu. Haka kuma a sauran yankuna, akwai tsaunuka da koguna, irin su Tsaunin Tilla da Tsaunin Marama da Tsaunin Filato da dabbobin daji daban-daban.
Daga shafi na 493 zuwa na 693 kuwa, akwai rataye, da jaddawalin adadin kalmomin da aka yi amfani da su a littafin. Haka kuma akwai sauran muhimman bayanai da suke like da littafin.
Babu shakka littafin nan wani muhimmi ne kuma gagarumin aiki ne da zai dade yana amfanar al’umma. Dalili ke nan ya sanya Farfesa Sa’ad Abubakar ya ce: “Littafin Tarihin Biu ya bijiro da ingantaccen tarihin al’ummar Biu, wanda ya dangaci al’adu da zamantakewa sannan ya zayyano irin fadi-tashi da gwagwarmayar da yankin ya kutso a zamunna daban-daban. Ya kuma bayyana irin muhimman al’amura da suka shafi arzikin kasa da na al’umma da suka rika gudana a yankin na tsawon sama da shekara 400.
“Littafin nan babbar gudunmawa ce ga rumbun tarihi…ya dace duk wani dakin karatu da ya amsa sunansa, ya zamanto yana dauke da shi…ina shawartar al’umma da babbar murya, cewa kowa ya mallaki kwafin littafin nan.”