✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NATO ta yi alkawarin ci gaba da bai wa Ukraine makamai a yakinta da Rasha

NATO ta alwashin ci gaba da bai wa Ukraine makamai don yakar Rasha.

Kungiyar Tsaro ta NATO ta sha alwashin ci gaba da bai wa Ukraine taimakon makamai a yakin da ta ke yi da Rasha.

Alkawarin na NATO na zuwa ne bayan Finland ta shafe gomman shekaru tana kin ba da goyon baya wajen gina shingen tsaro a kan iyakar Rasha karkashin wani hadin guiwa na ‘yan ba ruwanmu, amma a yanzu ta sake salo, lamarin da ya bakanta ran gwamnatin Kremlin.

A bangare guda, Rasha ta sanar da kaddamar da hare-haren jiragen sama a gabashin Ukraine da kuma birnin Lviv da ke yammacin kasar a can kan iyaka da Poland.

A wani taron ministocin harkokin waje da ya gudana a birnin Berlin, Ministar Harkokin Wajen Jamus, Annalena Baerbock ta ce, za su samar da tallafin soji ga Ukraine muddin kasar na cikin bukatar haka domin kare kanta.

Shi ma Sakataren Kungiyar Tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg, ya ce Ukraine za ta iya samun galaba a wannan yakin, ganin yadda ‘yan kasar ke ci gaba da nuna jarumta wajen bai wa kasarsu kariya.

A ranar Litinin ne ake sa ran ita ma Sweden za ta bi sahun Filand domin zama mamba a kungiyar tsaron ta NATO duk kuwa da korafin da Turkiyya ta yi na cewa, kasashen Sweden da Filand din na bai wa mayakan Kuradawa masu tsattsauran ra’ayi mafaka.