Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce za a samu rigakafin kwayar cutar COVID-19 kafin karshen wannan shekarar.
Darakta-Jananr na WHO, Tedros Ghebreyesus ya sanar da haka a ranar Talata, sai dai bai yi karin haske ba.
“Ana bukatar samun rigakafi kuma ana kyautata zaton kafin karshen bana zai samu. Akwai kyakkyawan fata”, inji shi.
Kamfanin dillancin labaru na Reuter ta ruwaito Ghebreyesus na bayyana haka ne a taron Majalisar Amintattun hukumar kan COVID-19.
Kawo yanzu magungunan rigakafin cutar guda tara ne hukumar za ta fara gwajin su da nufin raba guda biliyan biyu a 2021.