Aminiya: Ka gabatar mana da kanka?
Sunana Yahaya Ibrahim amma an fi sanina da Iya Mai Waina. Ina da shekara 28 zuwa 29. An haife ni ne a Jihar Kano a karamar Hukumar Dawakin Kudu. Daga baya ne na koma Jihar Kaduna inda yanzu haka nake da shekara 17 ina zaune a can.
Aminiya: Mece ce sana’arka?
Ina sana’ar sayar da waina ne, ma’ana ina toyawa kuma mutane na zuwa suna saye, wasu suna ci a shagona wasu kuma suna tafiya da ita (take away).
Aminiya: A ina ka samo sunan Iya, kamar yadda na ji wasu na kiranka?
Yadda aka yi na samu sunan Iya shi ne, akwai wata mata Bayarbiya ce da ke zaune a Kwanar Zango na Tudun Wada Kaduna, sai Allah Ya yi mata rasuwa da ma tana harkar sayar da waina ne, sai mutane suka ba ni shawarar me zai hana in gaje ta tun da ta rasu? Hakan ta sa na shiga sana’ar tare da wasu mata zaurawa, amma daga baya matan sun yi aure sai sana’ar ta sake tsayawa sai kuma yanzu da na sake samun shago a nan sai na cigaba. Sai dai yanzu ba tare da mata nake gudanar da wannan sana’a ba, na samu wasu maza ne da muke yin sana’ar tare, to ka ji yadda aka yi na fara sayar da waina, kuma sai mutane suka sanya mini sunan Iya Mai Waina.
Aminiya: A kullum kana samun nawa a wannan sana’a?
A gaskiya nakan yi cinikin Naira dubu 18 zuwa 19 don haka Alhamdulillah.
Aminiya: Kafin ka zo Jihar Kaduna, ka yi wasu sana’o’i ne kafin harkar waina?
kwarai kuwa, na yi sana’ar sayar da kayan abincin dabbobi na sayar da itace da kuma wasu buge-buge da ba a rasa ba.
Aminiya: Sana’ar waina tana bukatar jari mai kauri ne?
Ya danganta, amma in dai mutum yana son ya bude wajen sayar da waina yana bukatar ware Naira dubu 50 zuwa sama.
Aminiya: Wadanne nasarori ne ka samu a wannan sana’a?
Na samu nasarorin da suka hada da sanin manyan mutane a ciki da wajen Jihar Kaduna. Na yi suna a kafofin watsa labarai da suka hada da gidajen talabinin da rediyo na DITb da na Freedom da na Liberty da jaridar Aminiya da sauransu. Duk inda na shiga sai ka ji ana ga Iya Mai Waina. Sannan ko ba komai ina samun na rufin asiri a kullum.
Aminiya: Wadanne kalubale kuma kake fuskanta?
daya daga cikin kalubalen shi ne yadda da kyar na samu jarin da na fara wannan sana’a. Sannan yadda wasu ke daukata a matsayin dan Daudu.
Aminiya: Ka yi karatu mai zurfi kuwa?
Gaskiya a matakin firamare kawai na tsaya a bangaren boko, sannan a bangaren Islamiyya kuma na dan taba karatun addini daidai gwargwado.
Aminiya: bangaren iyali fa?
Gaskiya ban yi aure ba, sai dai akwai niyya.
Aminiya: Mutum nawa ke cin abinci a karkashinka a halin yanzu?
Akalla mutane shida ke cin abinci a yanzu haka a karkashina ta dalilin sana’ar sayar da waina. Ma’ana ina da yara shida da yanzu haka muke aiki tare da su.
Aminiya: Mene ne burinka?
Burina in bude babban shagon sayar da waina da na abinci. Sannan ina da burin daukar dimbin matasa aiki a karkashina.
Aminiya: Wane kira kake da shi ga matasa musamman masu zaman kashe wando?
Su tashi tsaye su rungumi sana’a komai kankantarta, zaman banza ba nasu ne ba.
Aminiya: Ya batun nuna maka kyama kasancewarka namiji mai sana’ar tuya waina?
Ka san mutane iri-iri ne. Wasu sun dauka sana’ar sayar da waina sai dan Daudu amma ni na dauke ta a matsayin sana’a ce mai muhimmanci. Bambancin dan Daudu da mai sana’ar sayar da abinci shi ne, shi dan Daudu an san shi da sanya kayan mata irin su zani da riga da kayan ado irin na mata kuma yana tafiya yana rangwada, amma ni ba haka nake ba, ba na sanya kayan mata kuma ba na yin rangwada. Kuma ko a Saudiyya mutane sun fi sayen abincin maza fiye da na mata. Ka ga kuwa da haramun ne namiji ya sayar da abinci, da kasar Saudiyya ta hana. Don haka ni ba dan Daudu ba ne, kamar yadda wasu ke zato.
Aminiya: Wane kira kake da shi ga gwamnati?
Ta rika tallafa wa masu kananan sana’a irinmu don ta haka ne arzikin kasa zai yalwatu a cikin al’umma.