✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya zata fara fitar da shinkafa kasashen waje- Ministan Noma

Ministan Albarkatun noma Alhaji Sabo Nanono, ya shaida cewa cikin shekaru biyu masu zuwa Najeriya zata fara fitar da shinkafar da ta noma kasashen ketare.…

Ministan Albarkatun noma Alhaji Sabo Nanono, ya shaida cewa cikin shekaru biyu masu zuwa Najeriya zata fara fitar da shinkafar da ta noma kasashen ketare.

Alhaji Sabo Nanono, ya shaida haka ne a mukalarsa da daraktan yada labarai na mai’akatar albarkatun noma Theodore Ogaziechi, ya gabatar a yau Talata a Abuja.

Ministan noman, ya ce noman shinkafa ya habbaka a kasar nan biyo bayan rufe kan iyakokin kasar nan na tudu inda a yanzu ake da manyan masana’artar sarrafa shinkafa 11 da zasu iya samar da tan 180 zuwa 350 a ko wace rana.