✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya za ta yi sabon mai horar da ’yan kwallo nan da mako biyu – NFF

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) Mista Amaju Pinnick ya ce nan da mako biyu Najeriya za ta samu sabon mai horar da kungiyar…

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) Mista Amaju Pinnick ya ce nan da mako biyu Najeriya za ta samu sabon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles.
Amaju Pinnick ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a garin Ibadan lokacin da yake yi wa manema labarai bayani.
Amaju ya ce za su yi kokari sosai domin tabbatar da cewa sun zabo sabon mai horarwa, sannan ya yi albsihir ga ’yan Najeriya cewa su tsammaci mai horarwa na kwarai.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) wanda ya ruwaito labarin ya ce Shugaban Hukumar NFF din yaje Ibadan ne domin kallon wasan Firimiya da aka buga a tsakanin kungiyar Ifenyi Uba da 3SC Shooting Star, wanda aka tashi kunnen doki da ci 2-2.
Game da gasar cin Kofin Duniya da za a gudanar a kasar Rasha, Mista Pinnick ya ce yanzu an samu ci gaba a harkar kwallon kafa domin haka kowace kasa tana da karfi sosai.
Ya kara da cewa: “An samu ci gaba sosai a harkar kwallon kafa. Peru ta lallasa Brazil a gasar cin Kofin Nahiyar Amurka (Copa America), duk da haka ina ganin muna da ’yan wasan da za su sa ’yan Najeriya su yi farin ciki.”
A fafutikar neman gurbin zuwa gasar cin Kofin Duniya da za a yi kasar Rasha dai kungiyar Super Eagles ta samu kanta a cikin rukuni mafi hadari na B, inda za ta fafata da kasashen Kamaru da Aljeriya da kuma kasar Zambiya.