Ministan a ma’aikatar man fetur ta Najeriya, Timipre Sylva, ya ce kasar ta bi sahun sauran kasashen nahiyar Afirka da ke Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur ta Duniya (OPEC) wajen rage yawan danyen man da take hakowa zuwa ganga miliyan 10 a kowace rana.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin taron kungiyar ta OPEC da wadanda ba mambobin kungiyar ba.
“Najeriya ta bi sahun sauran kasashen OPEC ne wajen rage yawan man da za ta hako zuwa ganga miliyan goma a kowace rana, daga watan Mayu zuwa watan Yuni na shekarar 2020, yayin da a tsakanin watan Yuli da Disamba 2020 za a rika hakar gangar danyan man miliyan takwas a kowace rana. Sannan za a fara hakar danyan man ganga miliyan shida a kullum daga watan Janairu na shekarar 2021 zuwa watan Afrilu 2022, kamar yadda aka sanar.”
A cewar shi ana sa ran idan aka cimma yarjejeniya kan yin hakan farashin man zai iya karuwa da akalla Dalar Amurka 15 a kan kowace gangar man a gajeren zango.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito ministan yana cewa wannan sauyin zai taimaka wajen zarta hasashen abin da za a samu kamar yadda yake a kasafin kudin da aka sakewa fasali.
“Farashin zai samar da karin kudin shiga, wanda ba zai gaza Dala biliyan biyu da miliyan 800 ba”, inji Mista Sylva.