Kocin Najeriya Super Eagles Stephen Keshi ya ce yana da yakinin Najeriya za ta haye matakin gaba a gasar cin kofin duniya. Ya ce duk da kunnen doki da kasar ta yi da Iran a ranar Litinin da ta wuce, kasar za ta iya samun nasara a kan sauran wasanninta biyu da suka rage mata a rukunin F.
Sai dai kocin ya zargi daya daga cikin ’yan kwallonsa Osaze a kan rashin tabuka abin a-zo-a-gani a wasan da Najeriya ta yi da Iran.
Ya ce da dan kwallon ya yi abin da ya kamata, da an samu nasara a wasan.
Kocin ya ce sukar da wasu ke yi masa na rashin doke Iran ba daidai ba ne don dama haka harkar wasa ta gada, wata ran ka samu nasara wata ran kuma akasin haka. “Duk abin da ka yi wasu ba sa gani don haka duk kushewar da ake min ba ta dame ni ba”, inji Keshi.
Sai dai ya bayar da tabbacin Najeriya za ta samu nasara a kan Bosniya a wasansu na gobe da shi new wasan da suka mayar da hankali a kai a halin yanzu.
Najeriya za ta haye mataki na gaba -Stephen Keshi
Kocin Najeriya Super Eagles Stephen Keshi ya ce yana da yakinin Najeriya za ta haye matakin gaba a gasar cin kofin duniya. Ya ce duk…