Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar, tashin gauron zabin da farashin man fetur ya yi a kasuwannin duniya zuwa sama da Dala 100 kowanne ganga guda, wata dama ce kasar ta samu ta cin gajiyar arzikin da Ubangiji ya wadata ta da shi musamman a karkashin sabuwar Dokar Man Fetur ta kasar.
Yayin da yake bude taron Masana Makamashi na Kasa karo 5 Buhari ya ce, hauhawan farashin man da aka samu irinsa na farko bayan faduwar da ya yi a watan Afrilun shekarar 2020, zai dada bude kofa ga masu zuba jari musamman ganin yadda gwamnati ta sake fasalin dokar man.
Shugaban wanda shi ne ministan man Najeriya ya ce domin cin gajiyar wannan dama, gwamnati ta aiwatar da sauye sauye da dama a bangaren man fetur da suka hada da sake fasalin kamfanin NNPC a matsayin kamfani mai zaman kan sa domin dogaro da kai da kuma zama irin sa mafi girma da kuma riba a Afirka.
Dangane cin gajiyar arzikin gas kuwa, Buhari ya ce za su ci gaba da inganta wannan bangare ganin yadda Allah Ya wadata kasar da arzikin da ya kai kusan triliyan 600 na ma’aunin cubic a karkashin kasa wanda zai taka rawa sosai wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.
Farashin gangar mai ya kai dala 110 a kasuwannin duniya
Farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya tashi zuwa Dala 110 kowacce ganga sakamakon fargabar da ake da ita na yakin dake gudana a Ukraine da kuma takunkumin karya tattalin arzikin da kasashen duniya ke kakabawa Rasha.
Rahotanni sun ce masu zuba jari da masu masana’antu na fargabar katsewar samun man a daidai lokacin da suke kokarin farfadowa daga annobar Korona wadda ta yi wa kasashen duniya illa.
A Larabar yau ake sa ran kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC ta gudanar da taro domin duba yadda za’a kara yawan man da ake kaiwa kasuwannin duniya domin daidaita farashinsa.
Irin wannan yunkuri a watan jiya bai haifar da da mai do ba, ganin yadda kasashen suka kasa cimma yarjejeniya a tsakaninsu na kara yawan man da suke hakowa kowacce rana.
Kasar Rasha da ke fuskantar takunkumin karya tattalin arziki, na daya daga cikin manyan kasashen da suka fi fitar da man zuwa kasuwannin duniya.