✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta lalace a mulkin APC —Secondus

Ya kamata Talakawan Najeriya su yi koyi da abin da ya faru a zaben Amurka, cewar Uche Secondus.

Shugaban jam’iyyar PDP na Kasa, Uche Secondus ya ce Najeriya ta lalace a mulkin jam’iyyar APC.

Secondus ya bayyana hakan ne a Karamar Hukumar Sagbama, Jihar Bayelsa yayin ba da tuta takara ga Henry Seriake.

Ya ce komai ya tabarbare a kasar ciki har sa tattalin arziki a mulkin APC.

Shugaban na PDP ya kara da cewa hanya mafi dacewa ita ce talakawa su zabi mutanen da suka dace domin jagorantar su a majalisa.

Secondus ya jagoranci ’ya’yan jam’iyyar ta PDP wajen nuna alhininsu kan kisan manoma 43 da Boko Haram ta yi a Zabarmari, Jihar Borno.

Shugaban jam’iyyar ya kuma ce ya kamata Manyan Hafsoshin Tsaro su san cewa Najeriya ta lalace a karkashin jagorancinsu.

Sannan ya sake jan hankalin Shugaban Kasa a kan kawo karshen ta’addancin da ake yi a jihohin Borno da Katsina.

A cewarsa, ya kamata jama’ar Najeriya su kaurace wa sake zabar APC a 2023, su yi koyi da irin abin da ya faru a kasar Amurka.