Najeriya na dab da samar da maganin cutar suga (Diabetes mellitus) daga shukoki na cikin gida.
Binciken masana ya gano ana iya yin maganin cutar suga daga kayan hatsi masu mai da ake nomawa a dukkanin jihohi a Najeriya.
Masana a Hukumar Bincike da Samar da Kayayyakin Masana’antu ta Kasa (RMRDC), sun gano cewa muhimman sinadaran da ke cikin kwayar gyada su ne Carbohydrate (kashi 10 zuwa 20 cikin 100), Protein (kashi 16 zuwa 36 cikin 100) da kuma maiko (kashi 36 zuwa 54).
Darekta Janar na RMRDC, Farfesa Hussaini Ibrahim ya ce shukar muhimmin abinci ne saboda karin sinadaran da yake dauke da su na coenzyme Q10, arginine, da polysterols.
Bayan haka tana dauke da calcium, iron, magnesium, phosphorus, manganese, sodium, potassium, zinc, copper da kuma selenium.
— Mece ce cutar suga?
Cutar suga da daga rukunin cututtuka da ke faruwa sakamakon matsala a hanyoyin jini, kuma take sanadiyyar yawan mace-macen masu ita.
Dakta Femi Ibidungba ya ce cutar na samuwa ne sakamakon raunin jiki wajen sarrafa sinadaran carbohydrate, fat da protein.
Hakan na faruwa ne ida aka samu karancin fitar sinadarin insulin ko karancin tasirantuwar jiki da shi.
Cuta ce mai tsanani da wuyar sha’ani wadda idan ta yi takan yi sanadiyyar lacewar zuciya da koda da kwakwalwa da kuma ido.
Ana gadon ta sannan yanayin rayuwa na da tasiri a wurin kamuwa da ita.
— Rabe-raben cutar suga
A yayin samuwar cutar diabetes, kwayoyin halittar jikin dan Adam ba sa iya narkar da suga yadda ya kamata saboda rauni ko karancin sinadarin insulin.
Ya ce nau’ikan cutar sun hada da T1DM da kuma T2DM wanda shi aka fi sani.
“Ana kiran T1DM cutar suga mai dogaro a kan insulin.
“Na biyu kuma ana kiran sa mara dogaro a kan insulin, wanda ke samuwa saboda gazawar jiki wajen sarrafi insulin da rage yawan sinadarin suga.
“Nau’i na biyun shi ne yawancin mutane a fadin duniya ke fama da ita”, inji shi.
Rashin magance ta ko jinyarta da kyau na iya haifar da makanta, mutuwar koda ko a yanke wa mutum kafa ko hannu da sauran matsaloli da za su yi mummunan tasiri na tsawon lokaci ga rayuwa.
— Manunfa samar da maganin a Najeriya
Darekta Janar din ya ce hukumarsa ta gudanar da binciken ne saboda samun karuwar masu cutar a Najeriya, domin a samar da maganinta mai sauki a cikin gida.
Ya ce binciken ya kunshi tantance tasirin shukar da ake amfani da ita a matsayin maganin gargajiya na ciwon suga, wajen rage yawan sukari a jikin dan Adam.
“Sakamakon da aka samu ya nuna yana da karfin rage yawan sukari da maiko a jiki, wanda hakan ya nuna za a iya amfani da shi wurin hada magajin cutar”, inji shi.
Saboda haka hukumarsa da hadin gwiwar sauran cibiyoyin bincike sun fara aikin ganin yadda nan gaba za a rubanya samar da maganin ya wadata a kasuwanni.
Ya ce tuni aka gabatar da sakamakon binciken kuma wasu kamfanonin hada magunguna a Najeriya sun bayyana aniyarsu ta fara kera maganin domin futarwa kasuwanni.
“RMRDC ta yi amannar cewa idan aka samar da shi a wadace da kuma tallata shi yadda ya kamata, Najeriya za ta samu karin kudaden shiga daga kasashen waje, baya ga karuwar ciniki da tattalin arziki a bangaren masana’antun magunguna”, kamar yadda ya ce.