✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta karbi ’yan gudun hijira 73,000 daga Kamaru

Ana samun karuwar 'yan cirani daga Kamaru.

Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijara da ‘Yan Cirani ta Najeriya NCFRMI, ta ce ta karbi ‘yan gudun hijarar Kamaru tare da yi musu rijisata su 73,000.

Aminiya ta ruwaito Kwamishinar Hukumar, Imaan Sulaiman-Ibrahim ce ta bayyana hakan a makon da ya gabata a wani taron kara wa juna sani game da yi wa ’yan gudun hijira da masu neman mafaka rijista a Abuja.

Ta ce “Rikicin siyasar Kamaru ya ki ci ya ki cinye wa tun 2016, kuma hakan ya janyo karuwar cin zarafin dan adam tare da asarar rayuka da dukiyoyi musamman a yankuna biyu na arewa maso yamma da kuma kudu maso yamma na kasar.

“Wani babban koma baya da rikicin ya haifar shi ne yadda aka rika samun karuwar ‘yan cirani daga Kamaru zuwa Najeriya amma a matsayin ‘yan gudun hijira, wadanda ya zuwa watan Yuni 2021 mun yi wa 73,000 rijista,

A gefe guda kuma, ta ce a kan samu ‘yan gudun hijirar da ba su gaza 3,000 daga Kamaru suna shiga Najeriya a duk mako.

Shugaban ta kuma jaddada bukatar da ake da ita ta ganin an kare sansanonin ‘yan gudun hijirar tana cewa da zarar an gaza hakan, to zai iya zama koma baya ga harkokin tsaron Najeriya.