✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta ɗauki mataki kan masu zuwa Masallaci da gajeren wando

Wannan dai guda ne daga cikin sauye-sauyen da mahukuntan ke kawowa a Azumin bana.

Saudiyya ta ce za ta fara cin tarar mazan da ke zuwa sallah Masallacin Harami da gajeren wando.

Hukumar da ke kula da Masallacin Harami na Makkah da Madina ce ta bayyana hakan, tana mai cewa hukuncin tarar riyal 500 zai tabbata a kan masu sanya gajeren wando a masallatan.
Kazalika, hukumar ta yi gargaɗi kan cuɗanya tsakanin maza da mata, inda take gargaɗin mata masu ibada da su riƙa sanya hijabin da ya dace.
Wannan dai guda ne daga cikin sauye-sauyen da mahukuntan ke kawowa a Azumin bana, baya ga rage raka’o’in sallar tarawih da ta yi daga 20 zuwa 10.