✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya na neman taimakon MDD kan samar da abinci

Hadin gwiwar samar da wadatacce kuma lafiyayyen abinci a Najeriya.

Gwamnatin Najeriya na yin hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya domin samar da wadataccen abinci a kasar.

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya ce yin hakan wani yunkuri ne na kawar da yunwa da rashin abinci mai inganci, tare da rage cututtuka masu nasaba da rashin lafiyayyen abinci da dangoginsu.

Osinbajo, wanda shi ke jagorantar bangaren gwamnatin Najeriya a hadin gwiwar, ya ce wajibi ne a yi tsayuwar daka a kuma yi taron dangi domin samar da lafiyayyen abinci da kuma rage yadda yawancin mutane suke fama da karancinsa.

Ya bayyana wa taron tattaunawar hadin gwiwar ta Shirin Majalisar Dinkin Duniya kan Samar da Abinci a Abuja cewa hakan ya yi daidai da manufar Gwamnatin Shugaba Buhari na rage talauci a tsakanin mutanen Najeriya.

Bugu da kari, shirin ya dace da manufar Majalisar, a shirinta na tabbatar da samuwar lafiyayyen abinci da kuma shirinta  na Muradu Masu Dorewa na 2030.

“Wajibi ne mu fahimci cewa daukar kwararan matakai wajen inganta hanyoyin samar da abinci da kuma wadatuwarsa za ta bayu ga karuwar lafiyar yara da cigaban fikirarsu da kuma karfin basirarsu.

“Hakan kuma, zai yi tasiri waje kara musu hazaka a makaranta da kuma tasowarsu cikin koshin lafiya,” inji shi.