Najeriya ce ta zo ta 18 a cikin jerin kasashe 43 da suka shiga gasar tsere da tsalle-tsalle ta duniya da aka yi a Jihar Oregon da ke kasar Amurka.
Najeriya ta taka wannan rawar ce a lokacin da ake tsaka da fargabar cewar ba za ta tabuka komai ba a gasar baki daya.
- Hana sana’ar Acaba da hakar ma’adinai ba alheri ba ne —Action Aid
- Buhari zai tafi Liberia ranar Talata
Nasarar da ’yar tseren Najeriya, Tobi Amusan ta samu na lashe gasar gudun mita 100 mai gajeren zango, gudun da ta kammala shi a dakika 12 da digo 12, ya sa ta zo daya a duniya, wanda ya hakan fito da sunan kasar.
Amusan ita ta ciwo wa Najeriya lambar zinarenta na farko a gasar, da har Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjina mata tare taya ta murna.
Sai kuma Brume, wacce ta yi rawar gani a gasar tsalle mai dogon zango wacce ta samar wa kasar lamabar azurfa.
A karshen gasar wasannin baki daya, Najeria ta zo ta hudu a nahiyar Afirka. Yayin da ta ke bin bayan kasashen Kenya da Habasha da kuma Uganda.
A Nahiyar Afirka, kasar Habasha ce ke kan gaba a matsayi na 2 da lambar zinare 4, yayin da Kenya ta zo ta 3 nahiyar.
Kasar Uganda ita ce ta zo ta 14 a jerin kasashen da ke da yawan lambobin da suka ci a gasar.
Mai masaukin baki Amurka, ita ta lashe lambar gwal 13 wanda ya kai jimillar lambobin da ta samu na azurfa da tagulla 33, fiye da kowacce a duniya a gasar.
Gasar da aka soma a ranar 15 ga wata, an kare ta ce a ranar Lahadi, 24 ga watan Yuli.