✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAJERIYA A YAU: Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Tsarin Mulkin Najeriya?

Ko kun san tanadin da kundin tsarin mulkin ƙasa ya yi game da Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa da ayyukansa da alhakin da ya rataya a…

More Podcasts

Ko kun san tanadin da kundin tsarin mulkin ƙasa ya yi game da Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa da ayyukansa da alhakin da ya rataya a wuyansa?

Kundin na tsarin mulkin ƙasa shi ne dai kundin dokoki mafi ƙarfi a Najeriya wanda ya ƙunshi tanade-tanade a kan dukkan al’amuran da suka shafi alhakin da ya rataya a wuyan shugabanni da ma al’ummar ƙasa.

Kuma kamar yadda ya tanadi yadda ake gudanar da dukkan al’amuran ƙasa, haka ya ayyana ƙarfin ikon da kowane shugaba yake da shi, da iyakarsa da ma yadda zai iya miƙa wannan ƙarfin iko ga wani don gudanar da ayyukansa.

Shin wanne aiki takamaimai kundin tsarin mulki ya bai wa Mataimakin Shugaban Ƙasa?

Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan