More Podcasts
Domin sauke shirin latsa nan
Tun bayan da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa dan takarar shugabancin kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu bai mika mata takardun shaidar karatunsa ba ake ta ce-ce-ku-ce a kan lamarin.
Wannan dambarwa ya yi kama da wanda ya nemi tadiye Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2015.
- NAJERIYA A YAU: ‘Yadda aka kwakule min idanu da wuka’
- DAGA LARABA: Halin da karatun Boko ke ciki a Jihar Bauchi
Shin wane tasiri takardun shaidar kammala karatu ke da shi ga mai neman shugabancin kasa?
Wane irin kwali ake bukata shugabannin siyasa su mallaka? Wane muhimmanci yake da shi ga samun nasarar shugaba?
Wannan shi ne batun da shirin namu na yau ya mayar da hankali a kai.