✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nafisa ta lashe Gwarzuwar Jaruma a birnin Landan

Shahararriyar jarumar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta lashe lambar yabo ta Gwarzuwar Jaruma a yayin da aka gudanar da Gasar African Films Awards ta shekara…

Shahararriyar jarumar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta lashe lambar yabo ta Gwarzuwar Jaruma a yayin da aka gudanar da Gasar African Films Awards ta shekara 2017.

An gudanar da bikin gasar ne a birnin Landan a daren Asabar din da ta gabata, inda jarumi Ali Nuhu da Ramadan Booth suka samu halarta.

 “Lambar yabo ta 16, zan kuma ci gaba da kirge,” jarumar ta rubuta a shafinta na Twitter jim kadan bayan ta karbi lambar yabon a birnin Landan.

Jarumar wadda ta fito a manyan fina-finai da suka hada da ‘Guguwar So’ da ‘dan Marayan Zaki’ da kuma ‘’Ya Daga Allah’ ta jaddada cewa wannan lambar yabon da ta karba a Landan tana da matukar muhimmanci a gare ta, duk da cewa ba wannan ne karo na farko ko na biyu ko ma na uku da ta kai ga lashe gasar gwarzuwar jaruma ba.

“Ba wannan ne karo na farko ko na biyu ko ma na uku da nake lashe lambar yabo ba, amma wannan (ta Gasar African Films Awards) ta kasance mai matukar muhimmanci a gare ni. Alhamdulillah…. idan har ka san ka taimaka mini ta kowane fanni har na kai matakin da nake kai a yau, to wannan lambar yabonka ce.” Inji jarumar.

Jarumar ta kuma gode wa masoyanta da suka kasance tare da ita a lokacin da take hawa tudu da gangare a masana’antar fina-finan Hausa.

 “Ga masoyana, ku na musamman ne a wurina, babu abin da ya fi ku, na rantse muku, soyayyarku gare ni ta daban ce, ba ta da mahadi, so ne na hakika da babu algus ciki, Ina kaunarku.”