✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nadin Halima Atete sarautar ‘Gimbiyar Kannywood’ a Zamfara ya bar baya da kura

Nadin sarautar Gimbiyar Kannywood da kungiyar Arewa Filmmakers Association of Nigeria (AFMAN) reshen Jihar Zamfara ta ce, masarautar Gusau ta yi wa fitacciyar jarumar fina-finan…

Nadin sarautar Gimbiyar Kannywood da kungiyar Arewa Filmmakers Association of Nigeria (AFMAN) reshen Jihar Zamfara ta ce, masarautar Gusau ta yi wa fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Halima Atete a Gusau kwanakin baya, ya bar baya da kura, kasancewar a yanzu masarautar ta tabbatar da cewa ba ta nada jarumar wata sarauta ba.
Masarautar ta musanta batun nadin ne ta bakin sakatarenta, Alhaji Sambo A. Sambo a lokacin da yake yi wa Aminiya karin bayani, inda ya bayyana cewa masarautar tana gudanar da bincike, kuma za ta dauki matakin kotu a idan ta gamsu an yi mata kage ne.
Idan ba a manta ba a watan jiya ne kungiyar AFMAN reshen Jihar Zamfara ta shirya bikin nada Shugaban kungiyar Arewa Filmmakers Association (AFMAN), reshen Jihar Kano, Jamilu Yakasai sarautar Saradaunan Kannywood da kuma jaruma Halima Atete sarautar Gimbiyar Kannywood.
Taron dai ya gudana a karkashin kungiyar AFMAN reshen Jihar Zamfara ne ba tare da kuma an ga tawagar Sarkin Gusau Alhaji Ibrahim Bello a wurin nadin ba.
Da yake gabatar da jawabinsa shugaban kungiyar reshen Jihar Zamfara Alhaji Sani Garba Gusau ya bayyana sun yi wadannan nade-nade ne sakamakon la’akari da irin gudunmawar da wadannan jarumai suke bayarwa ga ci gaban Kannywood.
Ya kuma tabbatar da cewar gogewa da kuma sadaukar da kai na wadannan mutane ne sanadiyyar yi musu wadannan sarautu, “Mun zabo wadannan mutane da aka nada ne daga Borno da Kano da Katsina da sauran garuruwa.”
Ya alakanta rashin halartar Mai martaba Sarkin Katsinan Gusau wurin taro ne sakamakon umara da ya je a Saudiyya, inda ya tabbatar wa wadanda aka nada din cewa da zarar Sarkin ya dawo za a gabatar da su domin ya sa musu albarka.
Gimbiyar Kannywood Halima Atete ta bayyana farin cikinta bisa nadin da aka yi mata.
“Wannan nadin ya tabbatar mini da kwazon da muke nunawa a Kannywood. Don haka na yi matukar farin ciki, kuma na sanya hakan a cikin manyan abubuwan tarihin da ba zan taba mantawa da su a rayuwata ba,” inji ta.
Sai dai duk da ruguntsumin nadin da aka sha, Sakataren Majalisar Masarautar Gusau, Alhaji Sambo A. Sambo ya ce masarautarsu ba ta da masaniya kan wadannan nade-nade da aka yi.
Ya ce: “Wadannan nade-nade ba daga masarautarmu ba ce, domin ni ban sani ba, ka ga kuwa a matsayina na Sakataren Masaurautar Gusau ba za a yi nadin da ban san da shi ba.”
Alhaji Sambo ya bayyana cewa wani daga cikin furodusoshin Jihar Zamfara mai suna Idris, ya zo ya iske shi, sannan ya nuna masa jerin sunayen mutanen da ya ce kungiyarsu tana so ta nada sarauta. “Na ce ban gane a nada ba, ya ce, su matsayinsu na Arewa Film Producers da ke Zamfara su suke so su yi nadin, sai na tambaye shi, lambar yabo za su bayar ne ko nadin sarauta? Domin akwai bambanci a tsakanin ba da lambar yabo (award) da kuma nadin sarauta, babu yadda za a yi nadin sarauta sai a cikin fada, ya ce mini wancan nadin sun yi a Sakatariyar JD. Kuma kowa shaida ne Mai martaba bai je ba, saboda Mai martaba ba ya zuwa nadin kowace sarauta idan ba a cikin fada ba,” inji shi.
Ya ce bayan ya kawo jerin sunayen ne sai ya ce masa babu yadda za a nada wani sarauta sai da yardar masarauta.
Sakataren ya kara da cewa: “Ana cikin haka sai Rashida Adamu (Mai Sa’a) ta bugo mini waya, ta ce an ce za a nada ta sarauta, ta sanar da ni ta shaida wa Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Ganduje da Shugaban Majalisar Jiharsu da sauran mukarraban gwamnati batun nadin da za a yi mata, kuma sun ce za su zo. Ta ce ta kuma buga katin gayyata, sai Idris ya sake samuna, na ce masa ai ba haka aka yi ba, a ina a duniya aka taba yin haka? Yaya gidan sarauta zai nada mutum bai san shi ba, bai san mene ne halayensa ba? Ba a yin abu a duhu. Na ce wa Rashida ban san da batun nadin sarautarta ba, amma za ta iya zuwa, bayan ta zo wurinmu, ta nuna mini katin gayyatar nadin sarautar. Muka je ta ga Mai martaba, ta yi bayani, sannan ya sanya mata ranar 30 ga watan Yuli, daga baya ne tawagar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kawo mana ziyara, sannan suka sanar da mu ranar 30 ga Yuli za a yi zabe a Kano, don haka ba za su samu damar zuwa nadin sarautar ba, suna neman a daga, hakan ya sanya aka mayar da ranar 6 ga Agusta a matsayin ranar nadin. Masarauta Rashida kawai ta sani,” inji shi.
Dangane da matakin da masarauta za ta dauka a kan batun nadin, sai ya ce tuni masarautar ta fara gudanar da bincike a kan al’amarin. “Masarauta ta bukaci fitaccen dan kasuwar fina-finan Hausa, Alhaji Sani Rainbow ya nemo jaridun da suka buga labarin nadin sarautar ba tare da yin kwakkwaran bincike ba. Idan muka ga jaridun sai mu gudanar da bincike don mu gano suna da laifi ko akasin haka. Sai mun gudanar da bincike za mu fahimci ko za mu dauki matakin zuwa kotu ko a’a,” inji shi.
Aminiya ta tuntubi jaruma Halima Atete ko me zai ta ce a kan wannan al’amari, sai ta bayyana cewa a halin yanzu ba za ta iya cewa komai ba.