✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Nada Sarki Sanusi Khalifan Tijjaniyya alheri ne —Shehunnai

Shehunan Tijjaniyya sun umarci mabiyan darikar su yi alfahari da zaman Sanusi II Khalifa.

Shugabanin Darikar Tijjaniyya a Najeriya, sun bayyana nada tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, shugaban darikar a Najeriya, da cewa ‘albarka’ ga daukacin Najeriya baki daya.

Shehunan sun bayyana hakan ne yayin da suka kai wa Sarki Sanusi II ziyara a gidansa da ke Kaduna, inda suka umarci mabiya darikar da su yi alfahari da nadin nasa.

Wakilin Shugaban Tijjaniyya na duniya, Sheikh Abdul-Ahad Nyass, ya bayyana nadin tsohon Sanusi II a matsayin saka kwarya a gurbinta.

Ya kuma bayyana cewa shugaban Tijjaniyya na duniya baki daya, Sheikh Mahi Nyass na alfahari da irin nasarorin da Sarki Sanusi II ya samu a rayuwarsa.

Ya kara da cewa taron dubban mabiyansu da aka yi a Kaduna, wata hanya ce ta martaba nadin da aka yi wa tsohon sarkin.

Shi ma da yake nasa jawabin, Sheikh Mukhtar Adhama, ya bayyana cewa zaman Sarki Sanusi Khalifan Tijjaniniya zai taimaka matuka wajen samar da ilimi mai fa’ida ga mabiyan darikar.

A jawabinsa, Sarki Sanusi II, ya bayyana yadda ya ziyarci ‘Kaulaha’ wanda a nan ne shehunan malamai suka tabbatar masa cewa zai yi sarautar Jihar Kano.

Ya ce duk da cewar kaso 80 na mabiya darikar sun yi amanna da nadin nasa, amma wanda suka jajirce tare da tabbatar da nadin nasa wasu shehunan malamai ne da bai ma san da su ba.

Ya yi fatan samun zaman lafiya a Najeriya da kuma hadin kan mabiya darikar Tijjaniyya a Najeriya da ma duniya baki daya.

Khalifan na Tijjaniyya ya ce duk da cewar ana cikin wani yanayi na matsi, amma a hankali komai zai dawo yadda ya kamata.