Hukumar kula da masu ciwon AIDS ta kasa (NACA), ta ce idan har ba a samu tallafi daga waje ba, Najeriya za ta kashe Naira biliyan 50 wajen sama wa masu cutar magani.
Shugaban hukumar, Dakta Gambo Aliyu, a hirarsa da Aminiya, ya ce, suna kashe Naira 50,000 a maganin duk mutum daya da ke dauke da cutar a shekara.
- Buhari ya yi wa malamai karin albashi da shekarun aiki
- Kotu ta aike da matashi gidan kaso bisa zargin fyade
Ya ce, “A yanzu haka muna da jerin sunayen masu karbar magani fiye da miliyan daya.
“Idan yau tallafin da ke zuwa daga PEPFAR na Gwamnati Amurka da Global Fund ya tsaya, Najeriya za ta ci gaba da biyan kudin maganin sama da miliyan daya.
“Ba kananan kudi ne ba a kashe naira 50,000 a kan duk mutum daya bisa la’akari da yadda muke siyo maganin dangas.
“Muna bukatar Naira biliyan 50 don yin magani ga mutane miliyan daya da ke dauke cutar HIV a shekara”, kamar yadda ya bayyana.
Ya ce, gwamnati da taimakon wasu masu ruwa da tsaki na kokarin samar da gidauniyar da za ta rika kulawa da masu cutar.