✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NABTEB ta saki sakamakon jarrabawar NBC/NTC na 2022

Kashi 69.6% na wadanda suka rubuta jarrabawar sun samu makin 'Credit' a darussa akalla biyar, ciki har da Ingilishi da Lissafi.

Hukumar shirya jarrabawa ta NABTEB, ta saki sakamakon jarrabawar NBC da NTC na 2022 da aka rubuta.

Shugabar hukumar, Farfesa Ifeoma Isiugo-Abanihe ce ta sanar da hakan yayin taron manema labarai da suka shirya ranar Laraba a Benin.

Da take jawabi ta bakin wakilinta kuma darakta a hukumar, Dokta Obinna Opara, ta ce mutum 87,668 ne suka rubuta jarrabawar a cibiyoyi 1,656 a fadin Najeriya da kasar Kwaddibuwa.

Farfesa Isiugo-Abanihe ta ce, lura da jimillar wadanda suka rubuta jarrabawar, an samu kari a yawan wadanda suka rubuta jarrabawar a 2021 da kashi 4.99 cikin 100.

Ta kara da cewa, mutum 58,569 (kashi 69.6 cikin 100) daga cikin wadanda suka rubuta jarrabawar sun samu makin ‘Credit’ darussa a akalla biyar, ciki har da Ingilishi da Lissafi.

Ta bayyana cewa duk da haka, kokarin da dalibai suka nuna a jarrabawar bara ya zarce na bana idan aka yi la’akari da yanayin darajar makin da suka samu.