✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Na yi nadamar mai da kaina namiji’

Wata mata da ta sauya halittarta zuwa namiji mai suna Debbie Karema ta ce a yanzu da ta gane kurenta, ta yi nadamar abin da…

Wata mata da ta sauya halittarta zuwa namiji mai suna Debbie Karema ta ce a yanzu da ta gane kurenta, ta yi nadamar abin da ta aikata.

Debbie Karema mai shekara 61 wacce ta fito daga birnin Hemel Hempstead a Gundumar Hertfordshire ta kasar Birtaniya, ta ce sauya halittarta zuwa namiji lokacin da take da shekara 44.

Debbie ta bayyana wa kafar labarai ta BBC cewa, bayan ta yi nadamar sauya halittar, yanzu haka tana son ta koma halittarta ta asali wato mace.

A yayin da take bayyana yadda aka yi ta koma namiji, Debbie ta ce, “Na koma namiji ne don a yarda da ni a duniya sannan kuma na huce wani takaici a lokacin ina yarinya.”

Debbie ta ce wani da ke matsayin uba a wajenta ya ci zarafinta ta hanyar yin lalata da ita lokacin tana karama, kasancewar suna zaune gida daya.

Ta ce hakan ya sa ta nemi mafita don sauya halittarta daga mace zuwa namiji inda ta tuntubi likitoci kuma aka yi mata tiyata ta koma namiji ta hanyar sauya mata al’aura zuwa irin ta namiji.

A lokacin da Debbie Karema ta koma namiji tana amfani da sunan Lee.

Bayan yin tiyatar sai ta sauya sunanta daga Debbie zuwa Lee, duk da yake tiyatar da aka yi mata a bangaren mafitsararta za ta iya kaiwa shekara 17 kafin ta warke, sannan halittar ta sauya yadda take bukata.

“Na yi tunanin zan shiga wani sabon yanayi na rayuwa, na koma wani irin mutum da halittarsa ta sauya kuma na yi hakan ne saboda na huce takaicina,” inji Debbie.

“Ina jin kamar ni mace ce, amma wacce aka yi wa sauyin jikin namiji kuma wannan sauyin halittar da aka yi min babban kuskure ne.”

A yayin da take bayani cikin nadama da takaici kan sauya halittar da aka yi mata ta ce, “A yanayin da nake ciki, duk da na huce takaicina kuskure na aikata babba.”.

A yanzu da ta kai shekara 61, Debbie na kokarin a yi mata tiyatar da za ta maido da halittarta ta asali zuwa mace.

Za a iya cewa, labarin Debbie na daya daga cikin abubuwa da dama da suke faruwa da mutane masu sha’awar sauya halittarsu ta hanyar amfani da Cibiyar Lafiya ta Kasa, (NHS) da Cibiyar da ke daukar nauyin kudin da ake kashewa kan kiwon lafiya a Ingila.

Wani kwararren likitan kwakwalwa mai suna James Caspian wanda ya dade yana samun masu irin wannan matsalar bayan sun sauya halittarsu daga baya su ce za su koma yadda suke tun asali, ya ce hadarin hakan ya fi faruwa ga mata.

“A wannan bangaren sauyin jinsi, har yanzu ana bincike kan maganin da za a iya bai wa masu larurar,” inji shi.

“Wadansu da yawa don an haife su a mata suna ganin kamar za a bar su a baya, ta yanayin jikinsu – cin zarafinsu da sauransu,” inji shi.