✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Na tausaya wa wadanda harbin Lekki ya shafa —Osinbajo

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya jajanta wa wadanda suka rasa rayukansu a harbe-harben da sojoji suka yi domin watsa taron masu zanga-zangar #EndSARS a…

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya jajanta wa wadanda suka rasa rayukansu a harbe-harben da sojoji suka yi domin watsa taron masu zanga-zangar #EndSARS a Lekki, Jihar Legas.

A jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Osinbajo ya ce ya ziyarci wadadan ke asibiti ziyara tare da addu’a kar hakan ta sake faruwa.

“Ina jajanta wa wadanda harbin Lekki ya rutsa da su da kuma ’yan sanda da sauran mutane maza da mata da suka rasa rayukansu a ’yan kwanakin da suka gabata a sassan Jihar Legas da wasu jihohi.

“Wasu asarar ba za a iya maye gurbinsu ba, amma za mu iya samu adalci a kan dukkansu.

“Ina tare da Legas da duk sauran jihohin da abin ya shafa a wadannan lokuta.

“Muna yin addu’a kada wadannan musibun suk kara farua. Allah ya albarkace ku duka, ’’ in ji shi.