✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na sayar da dana na saci yara biyar – Mai garkuwa da mutane

Wata mata ’yar shekara 28 da ake tuhuma da sace yara ta ce ta sayar da danta dan shekara hudu, sannan kuma ta saci wadansu…


Wata mata ’yar shekara 28 da ake tuhuma da sace yara ta ce ta sayar da danta dan shekara hudu, sannan kuma ta saci wadansu yara biyar, kafin asirinta ya tonu, aka kama ta.

Matar mai suna Joy Esu, ’yan sanda sun kama ta ce a Jihar Osun bisa zargin sace wani jariri dan wata 18 da haihuwa tare da hadin bakin wani mai suna Sidney Onwuka.

A yayin da wakilinmu ke tattaunawa da Joy, ta amsa laifinta cewa, ta taba sayar da danta dan shekara hudu, inda kuma ta sace wadansu yaran biyar ta sayar ga mutanen da take hulda da su. “Ni ban san abin da ya same ni ba. Wannan mutumin (Sidney) shi ne ya yaudare ni cewa in sayar da dana. Tun daga lokacin nan wannan halayya ta sayar da yara ta shiga kaina. Yakan tura ni in je in sato yara, kuma in tafi ba tare da na yi masa musu ba,” inji ta.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Osun, Mista Fimihan Adeoye ya ce mutanen da ake tuhuma za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.