✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na samu rufin asiri albarkacin kera takalma – Aminu Mai Takalma

Aminu Muhammad Saminaka Mai sana’ar kerawa da kuma gyaran  takalma a garin Saminaka da ke Jihar Kaduna, matashi ne da ya yi fice kan sana’arsa…

Aminu Muhammad Saminaka Mai sana’ar kerawa da kuma gyaran  takalma a garin Saminaka da ke Jihar Kaduna, matashi ne da ya yi fice kan sana’arsa ta hada takalma tare da gyaran takalman a yankin da kuma  kewaye. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya bayyana cewa  wannan sana’a ta yi masa komai. Don haka ya shawarci matasa kan su rungumi sana’a don kare mutuncinsu. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Wane lokaci ne ka fara sana’ar kera takalma?
Na fara koyon wannan sana’a ce tun shekarar 2003 a wajen maigidana a nan garin Saminaka. Na yi aiki da wannan maigida nawa har na tsawon shekara biyar da wasu watanni. Bayan ya yaye ni a shekarar 2009,  daga nan na zo na bude wannan shago nawa a shekarar 2010.
Aminiya: Kamar ta yaya kake yi wajen gudanar da wannan sana’a?
To yadda nake gudanar da wannan sana’a shi ne nakan tashi daga nan, na je Jos ko Kano na sayo kayayyakin hada takalman nan, na zo na hada na rika sayarwa da kwaya daya-daya wani lokaci ma har nakan bayar da sari.
Aminiya: Me ye ya karfafa maka gwiwar rungumar wannan sana’a?
Babban abin da ya karfafa mani gwiwar  shiga wannan sana’a shi ne yanayin rayuwa. Domin rayuwa a yau koda mahaifinka wani babba ne ko kuma kana ganin kai wani ne. Yana da kyau ka kama wata sana’a domin koda ka yi karatu, idan ba ka sami aiki ba, za ka iya yin wannan sana’a domin ka rufawa kanka da iyayenka asiri. Wannan shi ne abin da ya karfafa mani gwiwar rungumar wannan sana’a.
Aminiya: Daga lokacin da ka fara wannan sana’a zuwa yanzu wadanne irin nasarori kake ganin ka samu?
A gaskiya na samu nasarori da dama a wannan sana’a domin na yi aure da wannan sana’a na samu jari na sa yi mashin din hawa na biya wa kaina kudin makaranta da ‘yan uwana duk da wannan sana’a. Kuma ina da yara guda hudu da suke karkashina a wajen wannan sana’a.
Aminiya: Mene ne babban burinka kan wannan sana’a?
Babban burina kan wannan sana’a shi ne na kasance na karfafata ya zamanto ina yin takalma masu rufi. Bayan haka a yanzu haka na cika fom na makarantar koyon sana’ar kera takalma da jakankuna da huluna  da ke Zariya, domin na je na koyo tsari irin na zamani domin nazo na dada bunkasa wannan sana’a.
Aminiya: Mene ne bambancin irin takalman da kuke hadawa da irin takalman da ake shigowa dasu daga kasashen ketare?
Takalman da ake shigowa da su daga waje suna dauke da ranar mutuwarsu, kuma za ka samu sukan yi saman da kyau, amma kasan babu kyau. Mu kuma namu mukan sayo kayan ne mu hada shi gwargwadon amincinsa gwargwadon kudinsa.
Aminiya: Wanne irin tasiri ne kake ganin wannan sana’a take da shi wajen samar da ayyukan yi ga matasa?
Babu shakka wannan sana’a tana da tasiri wajen samar da ayyukan yi, domin tana hana zaman banza kuma matasa suna samun kaya a farashi mai sauki a wannan sana’a.
Aminiya: Wanne kira kake da shi zuwa ga gwamnati dangane da muhimmanci tallafawa irin wadannan kananan sana’o’i?
Kiran da zan yiwa gwamnati shi ne a duk lokacin da aka ga wani abu musamman irin wadannan kananan sana’o’i a tallafa masu, Domin akwai jama’a da dama wadanda sun iya irin wadannan sana’o’I, amma saboda rashin jari sun kasa gabatarwa da su. Don haka ina kira ga gwamnati kan ta rika bai wa masu kananan sana’o’i rancen jari domin su yi wannan sana’a su debi yara.