✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na samar wa matasa da dama sana’a ta dalilin fenti – Aminu Ibrahim

Aminiya: Ko za mu ji takaitaccen tarihinka? Sunana Aminu Ibrahim, amma ana yi mani lakabi da murmushin amarya. An haife ni a garin Dutsinma a…

Aminiya: Ko za mu ji takaitaccen tarihinka?

Sunana Aminu Ibrahim, amma ana yi mani lakabi da murmushin amarya. An haife ni a garin Dutsinma a ranar 22 ga watan Satumba na shekarar 1980. Na yi makarantar Firamare a Dutsinma, wadda na gama a 1991. Sai kuma Makarantar gwamnati ta jeka ka dawo da ke cikin garin Dutsinmar daga 1991 zuwa 1997. 

Sai na ji na fi sha’awar yin kasuwancin fiye da yin karatun tun da dama a gidanmu kasuwancin na tashi na ga ana yi, domin duk mako sai mahaifina ya tafi da ni nan kasuwar Dutsinma ina kama masa wasu ayyukan. Hakan ya sa tun ban fara fahimtar yadda ake yi ba har na fara ganewa. Kuma ko a lokacin da ina makaranta bai hana ni yin kasuwancin ba duk kuwa da kasancewar akwai yarinta, saboda ina sayar da irin ‘yan kayayyakin wasa irin namu na yara.

Aminiya: Wane irin kasuwancin ka ci gaba da yi bayan barin makarantar?

 Na cigaba da yin fatauci ne a nan kudancinmu, wato irin su Funtuwa, dandume da sauran irinsu, ina kuma sayo masara da sauran kayayyakin da ake sarowa daga wannan yankin ina kawowa Dutsinma ina sayarwa.

Aminiya: Mene ne dalilin yi maka lakabi da Murmushin amarya?

To dalilin wannan lakabi dai shi ne, a lokacin da nake yin yawon wancan fataucin daga baya kuma sai na canza wata sana’ar ko kuma yin kari a kan wadda ake yi. Kasan dan kasuwa kullum tunaninsa ina zai kara fadada harkar kasuwancinsa? To sai na fara sayar da kayan daki irin wadanda ake kai wa amare,. Irinsu gado da katifa da kuma kayan kyale-kyale na kawata dakin amarya. 

To su matan ne da kansu suka fara kawo wannan suna na murmushin amarya domin suna cewa duk dakin amaryar da aka sanya wa wadannan kaya lallai sai ta yi murmushi. Ni kuma jin wannan suna da matan suka cika ambatawa wajen shagon namu sai na ce to me zai hana mu dauki wannan suna mu yi amfani da shi? Ka ji dalilin samun wannan lakabi na murmushin amarya. Kuma tun sunan bai yi fice ba har yanzu sai muce muna kara yi wa Allah godiya.

Aminiya: Ba ka yi tunanin yin wata sana’ar hannu ba irinsu dinki ko saka da sauransu?

Gaskiya in baya ga noma ban koyi irin wadannan sana’o’i ba. Ba wai don bani iya su ba, a’a sai don lura da na yi cewar akwai karancin ‘yan kasuwa matasa da muke da su musamman a wannan jiha ta mu. Shi ya sa na rungumi kasuwancin na kuma jawo wasu na sanya. Kuma in baka manta ba, a baya na ce maka fatauci na kama yi da na bar makaranta. 

To wani abu da ya kara shiga cikin zuciyata shi ne shirin a koma gona da maigirma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo, musamman noman shinkafa. Na san lokacin da aka ce an hana shigowa da shinkafa a kasar nan mutane da dama ba su ji dadi ba, amma kuma a daya gefen sai na lura babu wadanda suka fara tunanin maganar inganta wadda za mu rika nomawa musamman daga nan Arewa, kowa maganarsa ta bangare daya ce, bai tunanin daya bangaren wanda da haka sauran kasashen da muke sha’awa suka ci gaba. 

A gaskiya ni ba noman shinkafar na yi ba, abin da na yi shi ne yaya za mu rika ingantata. To sai babban abin da nake ciki a yanzu wanda kuma ina iya cewa a yanzu nake tafiya daidai da zamani. Wato harkar Fenti. Ba wai shafen fenti nake yi ba kamar yadda wasu za su yi zato,a’a, ina yin fentin ne ni da kaina. 

Watarana ina zaune, sai kawai na ce shin shi wannan fenti ba mu iya yin sa a nan Arewa, dole sai mun fita uwa duniya mun sawo? Allah cikin ikonsa sai Ya yi wa abin albarka. A yanzu ina tabbatar maka irin alherin da wannan sana’a ko kasuwanci na fenti ya kawo mani gaskiya sai dai in kiyasta. Babba daga cikinsu shi ne na samarwa matasa da dama hanyar cin abinci wanda ya fara tun daga cikin masana’antar har zuwa waje da ma duk inda muke hulda da su, domin a dauka a sanya cikin mota kuma a sauke.

Aminiya: In na fahimce ka babu wata matsala kenan?

Babbar matsalarmu dai a wannan fannin bata wuce ta sinadarin(chemical) da ake amfani da shi, wanda muke yin karo da wanda ya lalace. Sai kuma karancin jari tunda ba karkashin gwamnati muke ba. Sai kuma kasuwa. Anan ne ma nake so inyi amfani da wannan dama domin yin kira ga gwamnati ta tallafawa masu sana’a. 

Yana da kyau gwamnati ta rika tallafawa irinmu domin ko ba komai muna dauke mata nauyin wani sashen na matasa da marasa aikin yi.