Hamshakin attajirin nan na Jihar Kano, Aminu Alhassan Dantata, ya ce daina jin dadin rayuwa, kuma ba shi da wani buri sama da cikawa da imani.
Attajirin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Mataimakin Dan Takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC, Kashim Shettima.
- Uwa ta aurar da ’ya ba tare da sanin mahaifinta ba a Kano
- NAJERIYA A YAU: Karin Kudi: Akwai Yiwuwar Daliban Jami’ar Maiduguri Su Daina Karatu
Ya ce ton tasowarsa, ya samu damar haduwa da mutane da dama, kuma ya kulla abota da jama’a a duka jihohin kasar nan.
Sai dai, ya ce a halin yanzu da walan gaske ya samu mutum 10 daga cikin abokan nasa da ke raye.
“Na karade jihohin Nijeriya, kuma na yi harkoki da jama’a a daukacin jihohin, na yi abokai da dama sai dai abin bakin cikin shi ne, da wuya in ambato 10 daga ciki wadanda ke raye.
“Gaskiya a yadda nake yanzu, lokaci kawai nake jira. Ina fata in bar wannan duniya da imani.
“Ina fata ban saba wa kowa ba a rayuwa, idan kuwa hakan ta faru, ina fata za a yi mini afuwa, ni ma na yafe wa duk wani da ya saba mini.
“A zuri’armu n i kadai na rage, inda nake rayuwa a tsakanin jikoki,” inji Dantata.
Daga nan, ya yaba da ziyarar da aka kai masa, kana ya yi addu’ar samun dauwamammen zaman lafiya ga Nijeriya da al’ummarta.
Tun da farko, Sanata Kashim Shettima ya ce ya je Kano ne ziyarar tuntuba tare da ziyarar dattijon don neman tabarraki a wani bangare na yakin neman zabensu a 2023.
A cikin tawagar dai har da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, kuma sun ziyarci dattawan jihar kamar su Alhaji Musa Gwadabe da Janar Lawal Jafaru Isah (mai ritaya) da Alhaji Tanko Yakasai a gidajen su.