✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na dade ina burin zama ’yar fim – Meenat Yola

Amina Yola wadda aka fi sani da Meenat Yola tana daya daga cikin jarumai mata da a yanzu tauraruwarsu ke haskakawa a masana’antar fina-finan Hausa…

Amina Yola wadda aka fi sani da Meenat Yola tana daya daga cikin jarumai mata da a yanzu tauraruwarsu ke haskakawa a masana’antar fina-finan Hausa da ake kira Kannywood. Ta yi fina-finai da dama duk da cewar ba ta dauki dogon lokaci a harkar fim ba. A tattaunawarta da Aminiya, ta bayyana dalilin da ya sa ta shiga harkar fim, burinta a harkar da kuma fatan da take da shi. Ga yadda hirar ta kasance:

 

Za mu fara da gabatar da kan ki, wace ce Meenat?

Sunana Amina Yola, sai dai an fi sani na da Meenat Yola, ni ’yar asalin Jihar Adamawa ce, amma na tashi a garin Ibadan da ke Jihar Oyo, a can na girma, na yi karatuna, kuma hakan ya faru ne sanadiyyar mahaifina soja ne, kuma a can ya yi zaman aiki, inda a yanzu da ya bar aiki muka dawo Arewa da zama, yanzu kamar shekara hudu ke nan da ta wuce.

To yaya aka yi kika samu kanki a harkar fim?

Ni dama tun ina karama ina da sha’awar harkar, to bayan mun dawo Arewa da zama sai na nemi yadda za a yi na shiga harkar fim din.

Ta wacce hanya kika shiga harkar?

Na samu shiga harkar fim ne ta dalilin wata kawata, duk da yake dai ita ba ’yar fim ba ce, amma tana da alaka da ’yan fim, don haka sai ta kawo ni wajen wani fitaccen dan fim, daga nan ya zame mini jagora a harkar, inda a yanzu ake damawa da ni a harkar.

A lokacin da kika shiga harkar da wane fim kika fara?

To, fim din da na fara yi dai shi ne ‘Wani Lokaci’ kuma Ibrahim Bala shi ne daraktan fim din.

Ganin cewar shi ne fim dinki na farko, ko yaya kika samu kanki a farkon lokacin aikin?

To, gaskiya da yake na san kaina a kan harkar, don haka ni ban ji wani abu ba, na san dai akwai wahala, amma da yake ina son abin ban ji faduwar gaba ba.

Daga loacin da kika shiga harkar fim zuwa yanzu akalla kin yi fina-finai nawa?

E, to, duk da dai ba zan iya kawo su duka ba saboda wadansu ba su fito ba, amma dai wadanda zan iya fadarsu a yanzu su ne kamar ‘Wani kauli da ‘Gidan Kitso’ da ‘Samun Duniya’ da ‘Matar Bahaushe’ da ‘Tuggu’ da sauransu.

A cikin fina-finan da kika fito wanne kika fi so?

To, gaskiya duk ina son su, amma dai idan za a ce na fitar da guda daya, to zan iya cewa fim din ‘Tuggu’ saboda shi ne fim din da na fito a matsayin jaruma, ba kamar sauran fina-finan ba, da wasu da nakan yi fitowa biyu ko uku ne.

Ganin cewar a yanzu kin zama cikakkiyar jarumar fim, ko yaya za ki kwatanta rayuwarki ta baya da kuma ta yanzu?

A gaskiya na samu canjin rayuwa sosai, domin ita harkar fim kamar wata makaranta take, duk yadda ka zo da iliminka to sai ka sake wani sabon karatu na rayuwa, saboda irin jama’ar da masana’antar ta tara, don haka akwai darasi na rayuwa a cikin harkar fim.

To idan muka koma baya kafin ki shiga harkar, ko yaya kike kallonta a wancan lokacin da kuma yadda kike jin labarinta?

A yadda nake kallonta da kuma yadda nake jinta, to akwai bambanci a da da kuma a yanzu da nake ciki, ka san ita harka ta rayuwa a yadda kake kallon abu da yadda kake jinsa a wajen mutane ba lallai ba ne ya zama daya da yadda lamarin yake.

Don haka na samu labarai da dama a game da ’yan fim, amma da na zo sai na ga abin ba haka yake ba, kuma ni ma abin da nake tunani da na shigo sai na ga ba haka yake ba, don haka ana fada min ’yan fim suna da girman kai, sai kuma da na zo cikinsu sai na ga ba haka abin yake ba, sannan kafin in fara fim, ina tunanin yadda za a hadu da manyan jarumai kuma yaya zan gan su. To sai kuma na zo muna tare da su, muna yin aiki tare, to abin sai ya burge ni sosai.

Da yake yanzu kin zama ’yar fim, ko za a iya cewa burinki ya cika tun da kin samu kanki a cikin abin da kika dade kina nema?

To ka san shi buri na rayuwa yana da yawa, don haka ta wani bangaren zan iya cewa burina ya cika, amma dai a yanzu ina son in zama fitacciyar jaruma kamar yadda sauran jarumai suka shahara a duniya.

Bayan harkar fim ko kina yin wata harka kamar kasuwanci?

Eh, gaskiya ina yi harkar kasauwanci na sayar da kaya, kamar atamfa da takalma da sauran kayan bukata na mata, kai har ma na maza ina sayarwa.

A rayuwarki me kika dauki harkar fim?

To, ni na dauki fim a matsayin sana’a, kuma ita sana’a mutum shi ne yake sarrafata yadda ya ga dama, idan ya so sai ya zama mutumin kirki kuma idan ya so sai ya zama mutumin banza.

Ko akwai wata rana da ba za ki taba mantawa da ita ba a zaman ki a masana’antar fim?

To, ni dai ina ganin ranar da ba zan taba mantawa da ita ba, ita ce ranar da aka fada mini zan yi aikin fim din ‘Tuggu’, domin ba zato ba tsammani sai kawai aka sanar da ni in fito gobe za mu je aiki, kuma da na je aka sanya ni a matsayin jarumar fim din, to gaskiya wannan ranar a bar alfahari ce a gare ni.

Ko akwai wata matsala da kika samu a harkar fim?

Gaskiya ba ni da wata matsala da kowa, don muna harkarmu da su lafiya, hakan ya sa duk lokacin da aiki ya samu in dai na dace da rol din, ko ina Kano ko na tafi Adamawa za a kira ni.

Wane buri kike da shi a game da harkar fim?

To, burina dai shi ne a yadda na fara harkar fim din lafiya, to ina fatan in gama ta lafiya, kuma ina fatan Allah Ya fito mini da miji nagari, in yi aure.