✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na ci na 50

Wata mata ce tana sana’ar cincin amma abin takaici, kullum idan ta ajiye cincin dinta idan gari ya waye sai ta ga cincin yana ragewa,…

Wata mata ce tana sana’ar cincin amma abin takaici, kullum idan ta ajiye cincin dinta idan gari ya waye sai ta ga cincin yana ragewa, har tafara zargin ko bera ne ke yi mata barna idan dare ya yi. Matar nan ta yanke shawarar yau ba za ta yi barci ba sai ta kama mai yi mata sata. Dare na yi can sai ta ji ana kurmusu, ana cin cincin cikin duhu. Matar ta dauko fitila, tana haskawa sai suka yi ido hudu da mijinta. Budar bakin gogan naka ke da wuya sai ya ce: “Na ci na hamsin.”
Daga Hafeez I. Sanda Katsina, 08164308607