Hkumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano ta dakatar da dukkanin ma’aikatan Asibitin Murtala Muhammad da suka yi aiki a ranar da wata mara lafiya mai suna Sha’awa Abdulmumini ta rasu ita da jaririn da ke cikinta.
Daukar matakin ya biyo bayan korafin da ’yar uwar marigaiyiyar mai suna Zainab Abdulmumin ta yi cewa sakacin ma’aikatan asibitin ne ya janyo rasuwar ’yar uwar tata.
- An fara zagayen karshe na sayar da tikitin kallon cin kofin duniya a Qatar
- APC ta dage fara yakin neman zaben Shugaban Kasa har sai abin da hali ya yi
Daraktan Harkokin Lafiya a Hukumar, Dokta Sulaiman Mudi Hamza, ya ce yanzu haka kwamitin ya dakatar da jagororin bangarorin da ma duk ma’aikatan da ke aiki a ranar da lamarin ya auku.
Matakin da muka dauka —Hukuma
Hukumar ta kuma ce bayan kafa kwamitin kwararu da za su binciko yadda lamarin ya faru, za ta dauki tsattsauran mataki kan duk wanda aka samu da laifi.
“Mun yi hakan ne domin samu a yi bincike mai zurfi, sannan mun zabo wasu ma’aikata daga asibitin da wajensa don su karfafa wa ma’aikatan gwiwar gudanar da aikinsu yadda ya kamata,” in ji shi.
Matar mai suna Sha’awa Abdulmumin, ta je Asibitin Murtala ne da ke Kano, lokacin da faya ta fashe mata, amma nakuda ba ta bayyana gare ta ba, domin samun kulawar likitoci, sai dai daga ita har dan da ke cikin, ba su bar asibitin da rai ba.
Yadda ’yar uwata da danta suka rasu —Zainab
’Yar uwarta mai suna Zainab da ke tare da ita tun daga zuwanta asibitin har zuwa rasuwarta, ta ba mu labarin yadda lamarin ya kasance.
“Ranar 2 ga Satumba, 2022 muka je asibitin saboda ruwa ya balle mata, amma babu nakuda.
“An shiga da ita dakin haihuwa, sai aka ce kwanciyar jaririn ba daidai take ba.
“Amma sai washegari da safe suka sanar da mu cewa dan ya mutu ba tare da an ciro shi ba, don haka za a yi mata aiki a cire.
“Sai suka ce sai mun kawo jini an kara mata, saboda ba ta da wadatacce a jikinta, muka je muka kawo.
“To fa bayan mun kawo jinin sai kuma muka shiga damuwa, saboda daga nan babu wanda ya sake bi ta kanmu; Karshe ma suka ce ai tun da dan ya riga ya mutu babu wani abin gaggawa a lamarin.”
Ta cgaba da cewa, “Daga nan ne na je na samu likitan da ke bakin aiki don jin lokacin da za a yi wa ’yar uwata aiki, sai ya shiga hantara ta da cewa ya riga ya yi tiyata uku a ranar don haka ba zai kara wata ba.
“Har da tambaya ta wai shi ya ce mu je mu nemo jinin da zan dame shi?
“Duk da haka ban hakura ba, na dinga bin sa cikin daren nan, amma hakarmu ba ta cim ma ruwa ba.
“Haka Sha’awa ta kwana da dan nan a cikinta, har sai da cikinta ya hau kumbura. Nan ma suka ce ta ciki take zubar da jin shi ya sa haka ta faru.
“Mun je Asibitin ranar Juma’a, amma har zuwa ranar Lahadi, ba a yi mata aikin ba.
“A ranar Lahadin ne Likitar da ta karbi aiki tayi mata, watakila don ita mace ce shi ya sa, amma dai ta nuna tausayinta kan lamarin.
“Bayan yi wa Sha’awa aikin ne aka kai ta dakin hutu (in da ake kai matan da suka haihu ko aka yi wa aiki bayan fito da su daga dakin haihuwa).
“Ta rasu ranar 5-ga Satumba, bayan an yi mata aiki an ciro dan, kuma ranar ne kawai likitar da take aiki, ta ba mu lokacinta ta yi mana bayani, ta kuma yi mana duk abin da ya dace, har aka yi mata aikin”, in ji Zainab.
Ta kuma bayyana mana cewa, ’yar uwar tata ta rasu ta bar ’ya’ya hudu, na biyar din ne kuma ta ga mu da ajalinta.
Matakin Masu ruwa da Tsaki
Kungiyar Lauyoyi Mata, da ta Lauyoyi ta Kasa (NMA) Reshen Jihar Kano da sauran kungiyoyi sun shiga lamarin, domin tabbatar da kwato wa Sha’awa hakkkinta.
A biyo mu ranar Juma’a domin jin cikakken bayani kan lamarin.