Mutumin nan dan kasar Denmark wanda ya yi zanen batanci ga Manzon Allah (SAW), wato Kurt Westergaard, ya mutu.
Iyalan Kurt Westergaard sun ce ya mutu ne bayan fama da doguwar rashin lafiya yana da shekara 86.
- Abduljabbar zai yi Babbar Sallah a gidan maza
- Zan tabbatar an hukunta wanda ya yi batanci ga Annabi – Tambuwal
Al’ummar Musulmin duniya sun yi ta tofin Allah-tsine ga ma’aikacin na jaridar Jyllands-Posten ta kasar Denmark kan zanen batancin da ya yi a shekarar 2005.
Batancin da Kurt Westergaard ya yi ga Manzon Allah (SAW), wanda kuma babban laifi ne a Musulunci, ya sa jakadun kasashen masu rinjayen Musulmi yi wa Denmark korafi, a yayin da Musulmi suka gudanar da zanga-zanga a sassan duniya.
Kariyar da Denmark ta ba shi a lokacin ya sa wasu Musulmi daukar matakin kaurace wa kayan kasar wadda ke tunkaho da fitar da madara zuwa kasuwannin duniya.
Wasu daga cikin masu tarzoma a zanga-zangar sun kuma kai hare-hare ga ofisoshin jakadancin Denmark.
An sha yi wa Kurt Westergaard barazanar kisa, lamarin da ya sa ya yi ta buya —amma duk da jami’an tsaon da aka ba shi, hakan bai hana yunkurin hallaka shi ba.
A 2011 gwamnatin Denmark ta yanke wa wani matashi da ya yi yunkurin kashe shi hukuncin daurin shekara tara, bisa zargin ta’addanci da yunkurin aikata kisa.
Daya daga cikin zane-zanensa 12 na batanci da kin jin Musulunci har da na rawanin bom.