“Alhaki,” inji masu iya magana, “kwikwiyo ne, yakan kuma bi mai shi”.
Hakan ce ta tabbata a kan wani mutum da ya kashe mai gidan da yake haya ya kuma boye gawarsa tsawon shekara da shekaru babu wanda ya gano, har sai da ya bayyana aikata hakan da bakinsa ga ’yan sanda.
- Fachi: Garin Barebari da ya zama kufai a saharar Nijar
- Jima’i ya zama wasan motsa jiki, za a yi gasar fidda gwaninsa a Sweden
Lamarin ya faru ne a garin Rosewel na Jihar New Mexico da ke Amurka a shekarar 2008, inda aka wayi gari da batar wani mai suna William Blodgett da aka fi sani da Bill, wanda ya yi batan dabo, aka neme shi sama ko kasa, aka rasa.
’Yan sanda tun a wancan lokaci sun yi iya bakin kokarinsu wajen binciko abin da ya faru, amma hakan ta faskara, suka kuma hakura suka bar maganar.
Kwatsam a rana tsaka a farkon watan jiya sai suka samu kiran gaggawa daga wani mai suna Tony Peralto dan shekara 37 da haihuwa, inda ya bayyana musu cewa, shi ne ya kashe Bill, wanda ya yi haya a gidansa.
Ya kuma bayyana hakan ne a yanzu saboda abin ya tsaya masa a rai, ya kuma dame shi matuka, inda dole ya fallasa abin da ya yi, inji shi.
“Mutane da yawa na da hujjarsu (na yin kisa). Ni dai ba ni da ita….. Gaskiya na kasa boye wannan abin da na aikata… Ni na gaji da wannan (masifar) rayuwar,” a cewar Tony a ofishin ’yan sandan Rosewel a lokacin tuhumar sa.
Tony ya yi wa ’yan sandan bayani dalla-dalla na yadda ya kashe Bill da makamin da ya yi amfani da shi da inda ya binne gawar ba tare da wanda ya gan shi ko kuma ya ci karo da da shi ballantana ya tona masa asiri tsawon wannan shekaru.
A ranar 3 ga watan Janairun 2009 ne wani mai suna Greg da ga Bill ya sanar wa ’yan sanda batar mahaifinsa bayan sama da kimanin kwana goma ba tare da jin duriyarsa.
A lokacin ’yan sanda sun yi ta binciken gidansa da unguwarsu da duk inda suke zaton ganin sa ko kuma jin labarinsa, amma abin ya ci tura.
Sai dai kasancewar motarsa a kofar gidan a ajiye ya kara daure musu kai kan lamarin.
Sai da Tony ya bayyana musu cewa, sun samu sabani ne da Bill ya kuma yi kokarin tashin sa daga inda ya ba shi haya.
Ganin ya takura masa sai kawai ya halaka shi, ya kuma binne gawar a wurin da ba a gano ba, sai yanzu da ya bayyana da kansa cikin kuka da takaici da kuma nadama.