✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutumin da ya hana Jamus amfani da Nukiliya a Yakin Duniya na Biyu ya rasu

Joachim Ronneberg dan asalin kasar Norway da bata shirin Jamus na amfani da Nukiliya a Yakin Duniya na Biyu ya rasu yana da shekara 99.…

Joachim Ronneberg dan asalin kasar Norway da bata shirin Jamus na amfani da Nukiliya a Yakin Duniya na Biyu ya rasu yana da shekara 99.

A  1943, shi ne ya jagoranci masu ma’aikatan sirri zuwa wani wajen da ake shirya makamin a yankin Telemark na Kudancin kasar Norway, inda suka lalata shirin.

Wannan jarumta da suka yi ya samu tagomashi matuka, wanda har Kamfanin Shirya Fina-Finai na Hollywood mai suna ‘Heroes of Telemark’, wanda Kirk Douglas ya jagoranta ya shirya fim kan haka.

Daga baya Ronneberg ya koma aiki da gidan rediyo a matsayin mai gabatarwa, inda yake yin shirye-shirye a kan matsalar yake-yake a tsakanin matasa.

Ya taba shaida wa BBC a shekarar 2013 cewa sai bayan da aka jefa makamai masu linzami a garuruwan Hiroshima da Nagasaki na kasar Japan a 1945, sannan ya gane muhimmancin kokarin da suka yi.

Firayi Ministan Norway, Erna Solberg ya shaida wa kafar Dilllancin labarai ta NTB cewa, “Yana daya daga cikin mazan jiya da muke girmamawa.”

Shi dai Ronneberg an haife shi ne a 1919 a garin Aalesund a kasar Norway, amma ya gudu daga Norway a 1940 bayan sojojin Nazi na Jamus sun kawo farmaki.

A lokacin yana da shekara 21 ya bar kasar tare da abokansa 8 a jirgin ruwa zuwa kasar Scotland.

A lokacin Jamus na shirya makamin nukiliya a yankin Rjukan da ke Telemark, sai Roneberg da wadansu abokansa biyar suka dawo, inda suka lalata shirin. Bayan sun bata makamin, sai suka sake guduwa zuwa Sweden da kyar duk da cewa sojojin Jamus 3,000 sun biyo su, amma suka kasa cim musu.

Wannan kokarin da suka yi da kuma farmakin da Amurka ta kawo wajen, shi ne ya tursasa Jamus ta gudu ta bar shirinta na hadawa da amfani da makamashin Nukiliya.