Akalla mutum shida ne suka riga mu gidan gaskiya, sannan uku suka jikkata a sakamakon hadarin mota da ya rutsa da su a Jihar Jigawa.
Hadarin ya auku ne a ranar Litinin da hantsi kan hanyar Hadejia-Kano cikin Karamar Hukumar Hadejia a jihar.
- Ba za mu fasa bincike ba duk da Mai Shari’a Tanko ya yi murabus —Majalisar Dattawa
- Mun lalata gonakin Tabar Wiwi 48 a Edo – NDLEA
Hadarin ya shafi wata mota kirar Lexus ce mai bakin launi, mai dauke da lamba AAA 153 EA, wadda aka ce ta dauko fasinjoji takwas masu rakiyar amarya daga Hadejia zuwa Yalleman.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da faruwar hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Talata a Dutse, babban birnin jihar.
A cewar jami’in, “Bayan da (Matafiyan) suka isa Gidan Sugar daga Hadejia, suna tsakar tafiya tayar motar ta fita, sai motar ta kwace wa direban ta wuntsila zuwa gefen hanya.
Ya kara da cewa, samun rahoton abin da ya faru nan take suka tura jami’ansu wurin don yin abin da ya dace, inda aka kwashi wadanda lamarin ya shafa zuwa Babban Asibitin Hadejia don yi musu magani.
Wadanda suka mutu daga ciki, “An mika gawarwakinsu ga ‘yan uwansu don yi musu jana’iza,” inji jami’in.
Kakakin ya ce, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Aliyu Sale Tafida, ya yi ta’aziyya ga ‘yan uwan wadanda suka rasu, kana ya jajanta wa wadanda suka jikkata a hadarin.
Kazalika, ya shawarci masu ababen hawa da su rinka kula da lafiyar tayoyinsu da sauran muhimman sassan abubuwan hawa kafin soma amfani da su a kowane lokaci.