Cibiyar Kare ’Yancin Nakasassu ta Duniya ta Sightsabers ta ce kimanin mutum miliyan 25 suke da nakasa a Najeriya.
Sightsabers cibiya ce da ke taimaka wa nakasassun da suke rayuwa a kasashe masu tasowa.
Cibiyar ta bayyana adadin masu nakasa a Najeriya ce ta bakin Ko’odinetanta na kasar Ghana da Najeriya, Dokta Sunday Isiyaku, yayin taron wuni biyu da aka shirya don horar da shugabannin kungiyoyin al’umma da Ma’aikatar Kare Hakkin Nakasassu ta Jihar Filato da kuma wata kungiyar kasar Austireliya mai suna Australian Aid suka shirya a otal din Crest Hotel da ke Jos a ranar Litinin da ta gabata.
Cibiyar wadda take da hedikwata a kasar Birtaniya da kuma rassa a kasashen Sweden da Norway da Indiya da Italiya da Jamhuriyyar Ireland da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da kuma Amurka ta bayyana cewa idan rayuwar nakasassu ba ta inganta ba, to rayuwar wadanda ba nakasassu ba ma ba za ta inganta ba.
Ya ce, “A Najeriya akwai kimanin mutum miliyan 25 da suke da nakasa, yawan mutane masu nakasa a Najeriya ya kai adadin yawan mutanen kasar Ghana miliyan 25, ba a ma maganar kasar Laberiya mai kimanin mutum miliyan hudu ko kasar Saliyo mai mutum miliyan shida.”
Dokta Isiyaku ya bayyana cewa yawan mutane masu nakasa a Najeriya ya fi yawan mutanen wasu kasashe masu yawa a duniya, don haka idan “Muka ki ba su kula ko muka nade hannuwamu don kin tallafa musu, to nan gaba hakan ba zai harfar mana da da mai ido ba,” inji shi.
Ya ce, “Idan da a ce ni dan siyasa da ke son zama Shugaban kasa ne, to zan mayar da hankalina kan mutum miliyan 25 da suke da nakasa a Najeriya, zan yi musu abubuwan da za su ji cewa su mutane ne, iya kuri’arsu za ta sa in zama Shugaban kasa, domin a iya sanina tunda ake zaben Shugaban kasa a Najeriya babu wanda ya taba samun kuri’a miliyan 25.”
A lokacin da yake jawabi a yayin taron, Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato ya bayyana taron horarwar zai sanya mutanen jihar su samar da wasu hanyoyin na tabbatar da zaman lafiya a jihar da ke fama da matsalar rashin tsaro.
Gwamna Lalong, wanda Mai ba shi Shawara na musamman kan Ayyukan kungiyoyi, Mista Irmiya Werr ya wakilta, ya kuma bukaci mutanen jihar su ba da hadin kai don ganin an gudanar da zaben kananan hukumomin jihar cikin lumana da kwanciyar hankali.