✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 7 sun mutu, 16 sun jikkata a hatsari ranar Sabuwar Shekara

FRSC ta ce hatsarin ya auku ne a dalilin gudun wuce hankali.

Akalla mutum bakwai sun mutu, wasu 16 sun jikkata sakamakon hatsarin mota a Ranar bikin Sabuwar Shekara a babbar Hanyar Legas-Ibadan.

Hatsarin ya ritsa ne da wata bas kirar Toyota Hiace da kuma tankar mai.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra (FRSC) na Jihar Ogun, Ahmed Umar, shi ne ya tabbatar wa manema labarai aukuwar iftila’in a Abeokuta, babban birnin jihar.

Umar ya ce hatsarin ya auku ne da misalin karfe 4:10 na yamma sakamakon gudun wuce hankali daga na direban bas din.

A cewarsa, hakan ne ya sa  bas din ta kwace wa direban inda ta daki tankar ta baya.

Ya kara da cewa, baki daya mutum 25 (maza da mata) hatsarin ya shafa inda mutum bakwai suka riga mu Gidan Gaskiya sannan 16 suka jikkata.

(NAN).