✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 663 sun kamu da COVID-19 a rana guda a Najeriya

A ranar Talata 9 ga watan Yunin da muke ciki ne aka samu adadi mafi yawa na mutane da suka kamu da cutar COVID-19 a…

A ranar Talata 9 ga watan Yunin da muke ciki ne aka samu adadi mafi yawa na mutane da suka kamu da cutar COVID-19 a Najerirya a cikin awa 24.

Mutum 663 ne suka kamu da cutar a ranar daga jihohi 26, adadi mafi yawa tun farkon bullar cutar a watan Fabrairu.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta ce hakan ya kai yawan wadanda suka kamu da annobar 13,464 a kasar.

Alkaluman na zuwa ne yayin da hukumomin kasar ke kara sassauta dokar kullen da suka sanya domin dakile yaduwar cutar ta coronavirus.

Zuwa daren Talatar mutum 4,206 sun warke daga cutar wadda ta yi ajalin wasu 365 a jihohi 35 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

COVID-19 wadda kawo yanzu mutum 8,893 ke fama da ita a fadin kasar ta fi kamari ne a jihohi uku.

Jihar Legas ce ke kan gaba wurin yawan masu cutar ta COVID-19 da mutum 6,065, sai Kano da 1,020, sannan Abuja da mutum 1,012.

Daga ciki a Legas an sallami mutum 944 suka warke, 497 a Abuja da kuma 275 a Kano.