Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC), ta ce mutum 61 suka mutu a haddura 33 da suka auku a sassan Jihar Borno tsakanin watan Mayu da Nuwamba, 2022.
Kwamandan hukumar a jihar, Utten Iki-Boyi ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a Maiduguri, babban birnin jihar.
- 2023: Ina da yakinin za a yi sahihin zabe – Jega
- ’Yan ta’adda sun kashe mutum 55,430 a Najeriya —Rahoto
Jami’in ya ce, daga cikin hadurran da suka auku, mutum 151 sun jikkata.
Ya kara da cewa, baki daya hadurran sun rutsa da mutum 285 ne da kuma motoci 46.
Ya ce, a Nuwamban da ya gabata mutum 37 ne suka mutu a hadurran da aka samu a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.
Iki-Boyi ya danganta aukuwar hadurran da gudun wuce kima da tukin ganganci da amfani da taya mara inganci da sauransu.
Daga nan ya gargadi masu ababen hawa, musamman masu motocin haya, da su rika amfanai da tayoyi masu inganci tare da kula da abubuwan hawansu yadda ya kamata.
(NAN).