✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 54 sun rasu a hatsarin jirgin kasa

Shi ne hatsarin jirgin kasa mafi muni cikin shekara 40 da suka wuce a kasar Taiwan.

Akalla mutum 54 ne suka rasu, wasu daruruwa kuma suka samu ranuka sakamakon wani mummunan hatsarin jirgin kasa.

Hatsarin ya auku ne bayan wani jirgin fasinja ya tunture daga sauka daga layin dogo a wata gadar karkashin kasa da safiyar Juma’a.

“Mutane sun yi ta karo da juna, wasu a kan wasu,” inji wata mata da ta tsallake rijiya da baya tana mai cewa, “Abin da ban tsoro matuka, wasu ma iyalai ne gaba daya a cikin jirgin,” mai tarago takwas.

Masana sun ce hatsarin jirgin kasan shi ne mafi muni a cikin shekaru 40 da suka gabata a kasar Taiwan, inji jirgin ke hanyarsa daga Taipei zuwa Taitung.

Masu aikin ceto sun garzaya zuwa wurin, inda suka yi nasarar kwashe daukacin mutanen da suka matale a cikin taragon jirgin kasar.